Uba ya kashe dansa saboda fitsarin kwance

0
115
Borno
Borno

An kama wani magidanci Jubrin Muhammad a Maiduguri babban birnin jihar Borno bisa tuhumar kashe ɗansa mai shekaru shida saboda fitsarin kwance.

Lamarin dai ya faru ne ranar 27 ga Yunin da ya gabata a unguwar Wulari dake birnin Maiduguri.

Mai unguwar Wulari, Bulama Lawan ya shaida wa wakilinmu cewa  mahaifin magidancin ne ya sanar da shi faruwar lamarin.

Ya ce “Wani Alhaji Mustapha ne ya yi min waya, ya ce min ɗansa Jubrin Muhammad ya kashe masa jika.

“Ya ce ɗan ya gwara kan jikan da bango har ya mutu.”

Bulama Lawan ya ƙara da cewa da ya je gidan domin tantance bayanin sai Jubrin Muhammad ya yi ta ba shi haƙuri ya na cewa tsautsayi ne ya faru.

Don haka sai ya kira ƴan sanda su ka tafi da shi.

Mai unguwar ya shaidawa wakilinmu cewa bayan ƴan sanda sun kama baban yaron ne ya tambayi kakan me ya jawo uba ya kashe ɗansa.

A cewarsa “kakan ya shaida min cewa yaron ya na fitsarin kwance ne.”

Kawo yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar Borno ba ta ce komai ba game da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here