Masarautar Zazzau ta dakatar da hakimi kan zargin lakada wa matashi duka

0
110

Majalisar Masarautar Zazzau ta dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah daga kujerarsa ta Marafan Yamman Zazzau.

Masarautar ta ce daukar matakin ya biyo bayan nazari koken da al’umman Unguwar Magajiya da ke birnin Zariya suka mika, wadda suka gabatar a gabanta na zargin cin zarafin al’umma da ake yi wa basaraken.

A takardar sanarwar da mai magana da yawunta , Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar ranar Talata, masarautar ta ce ta amince cikin gaggawa ta dakatar da Hakimin har sai abin da hali ya yi a nan gaba.

Shi dai Alhaji Mustapha, majalisar ta same shi ne da laifin zartar da hukunci da Hannunshi ne, ta wajen hukunta wani Yusuf Yahaya mazaunin Unguwar Magajiya wanda a bisa dokokin Shari’a da na Kasa ba shi da damaryi ko daukan haka, a cewar sanarwar.

Da kaukausar murya, a bisa ga wannan dakatarwar ga Marafan Yamman Zazzau, Masarautar tana jawo hankalin dukkan Hakimai da Dagatai da sauran masu rike da sarautar gargajiya cewar ba ta amince da su rinka daukar doka a hannunsu ba.

Majalisar Masarautar ta kuma kara tunatar da duk masu rike da sarautu a cikinta da su kiyaye cewan ba za ta lamunce da cin zarafi ko tozarta kowane irin jinsi na al’umma ba. Ta kuma kara jawo hankalin da a rinka mika wadanda ake tuhuma bisa laifuka ga mahukunta.

Daga karshe, Majalisan Masarautan Zazzau ta kara tabbatarwa al’umma cewar a kowane lokaci a shirye take domin daukan mataki mai tsanani ga duk wanda ya sabawa dokokin da Shari’a ta shimfida.

Sai dai da yake mayar da martani kan dakatarwar, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah ya ce ya sa an daki shi wanda ake zargin ne saboda ya kama shi yana luwadi ne da wani yaro a bayan gidansa kuma akwai wasu abubuwa da suke faruwa tsakaninsu.

Ya kuma zargi wasu ’yan majalisar Sarki da hannu wurin ta’azzara wannan rikicin.

A cewar shi, gudun bata sunan shi da na Sarkin Zazzau ne yasa ya dauki wannan matakin.

Ya bukaci da a gabatar da shi ne ga hukuma idan akwai bukatar hakan maimakon dakatar da shi da aka yi kawai, ba tare da binciken abin da ya sa ya dauki wannan matakin ba, kuma yanzu haka maganar na gaban ofishin ’yan sanda.

Dan haka wannan matakin da aka dauka an biyewa son zuciyar wasu ne kawai, a cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here