’Yan sanda sun kashe wanda ake zargi da fashi a Gombe

0
147

Rundunar ’Yan sandan jihar Gombe ta kashe wani da ake zargin dan fashi da makami ne ta kuma kama wasu mutum 3 da suka addabi mazauna jihar.

Ana dai zargin wadanda aka kama din da hana mazauna unguwannin Arawa, Malam Inna da Nayi-Nawa da ke birnin Gombe sakat.

A rahoton da rundunar ta fitar ta bakin Jami’inta na Hulda da Jama’ar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ta ce an sami nasarar ce a ranar 24 ga watan Yuni 2023.

Ya ce wasu gungun barayi ne suka shiga gidan wani attajiri da ke unguwar Arawa mai suna Alhaji Gidado Muhammad Sani, inda suka yi harbe-harbe.

A cewar Kakakin ’yan sandan, wadanda ake zargin sun kuma kwashe musu kayayyaki sannan suka ji wa mai gadinsa, Muhammad Abdullahi, rauni a kai da hannu da kuma bayansa.

A cewar sanarwar bayan sun samu kiran gaggawa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Oqua Etim, ya umarci rundunar ta musamman ta sintiri da  ta kai wa unguwar dauki inda aka fara ba-ta-kashi tsakanin ’yan sanda da barayin.

ASP Mahid ya ce nan take ’yan sanda suka yi nasarar kashe daya daga cikin barayin mai inkiya da Albaru dan unguwar Kumbiya-Kumbiya, suka kama wasu mutum uku.

ASP Mahid Mu’azu, ya ce bayan kama mutum 3, akwai wasu guda 6 da suka cika rigarsu iska da raunin harbin bindiga a jikinsu.

Har ila yau a wani labarin mai kama da wannan rundunar ta samun rahoton satar shanu, da wani kai suna Jibrin mazaunin kauyen Gidim ya kai rahoto ofishinsu na Yankin Gona a ranar 27 ga watan Yuni.

Ya ce wasu da ba a san ko su wane ne ba sun shiga masa gida inda suka yi awon gaba da bijiman shanunsa guda 2 da kudinsu ya kai ai Naira dubu 700.

Ya ce bayan samun rahoton ne suka shiga wani kango da ke unguwar Nasarawo inda suka gano shanun a ciki.

ASP Mahid ya ce suna bincike a kangon suka gano wata karamar bindiga kirar gida da harsasai, kodayake ya ce barayin sun tsere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here