Ƙarin ‘yan Najeriya miliyan huɗu sun shiga talauci – Bankin Duniya

0
129

Ƙarin ‘yan Najeriya kimanin miliyan hudu ne suka sake auka wa ƙangin talauci a cikin wata biyar na farkon wannan shekara saboda tsadar rayuwa, in ji Bankin Duniya.

Babban masanin tattalin arziƙi na bankin a Najeriya, Alex Sienaert, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a Abuja yayin wani nazari kan tattalin arziƙin Najeriya a cikin rabin shekara.

Katafariyar cibiyar hada-hadar kuɗin ta yaba da sauye-sauyen da Najeriya ke yi ciki har da cire tallafin man fetur da dunƙule kasuwannin canji da shugaba Bola Tinubu ya yi a baya-bayan nan, wanda ta ce zai iya alkintawa ƙasar kuɗi kimanin naira tiriliyan 3.9 ($5bn) a bana kaɗai.

Babban Bankin ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙin na da muhimmanci wajen sake farfado da tattalin arzikin Najeriya wanda tuni ya galabaita, ko da yake matakan na iya gigita al’amura cikin gaggawa ta hanyar haddasa ƙarin hauhawar farashi da tsadar rayuwa.

A cewar Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, sama da ‘yan Najeriya miliyan 130 ne wato fiye da rabin al’ummar ƙasar ke fama da talauci a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here