Gwamnatin Sakkwato ta fara biyan alawus din masu bukata ta musamman

0
151

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe na fara biyan alawus din Naira 6,500 duk wata ga nakasassu a jihar.

A wata sanarwar da sakataren yada labarai na gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar ya ce an biya kudin ne a lokaci guda a cibiyoyi daban-daban.

A cewarsa, “Cibiyoyi guda uku da suke Sakkwato ta Arewa, karamar hukumar Dange Shuni da kuma na karamar hukumar Gwadabawa ne aka yi rabon a cikinsu inda masu fama da bukata ta musamman suka fito sosai waje amsar alawus din wata-watan.”

Bawa ya ce gwamnan zai cigaba da yin hakan a yunkurinsa na rage wa masu fama da bukata ta musamman din wahalhalun rayuwa da saukaka musu domin rayuwa take inganta.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar da aka yi hira da su, sun jinjina wa gwamnan Ahmed Aliyu bisa farfado da tsarin ba su alawus din wata-wata.

Abubakar Suleiman, daya ne daga cikin masu cin gajiyar sharin daga cibiyar Sokoto ta arewa ya shaida ma wakilinmu cewa, tallafin zai dauki tsawon lokaci na taimaka wa rayuwarsu.

Ya ce, “Tabbas dawo da biyan alawus din wata-wata zai rage yawon barace-barace a kan titina da kwararo-kwararo,” ya shaida.

Gwamnan dai ya kafa kwamiti na musamman da aka daura wa alhalin tabbatar da an farfado da tsarin biyan alawus din a kowace wata domin kyautata rayuwar nakasassun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here