Cire tallafin mai: Abinci da sufuri na cinye albashin ma’aikata a Abuja

0
165

Da sanyin safiya, Mu’azu yake tashi daga gidan da yake haya da ya kama a kan Naira dubu 150 a yankin mararraba da ke iyakar Abuja da jihar Nasarawa, inda yake shiryawa ya fito domin neman motar tafiya wajen aiki.

Mu’azu Muhammad, ma’aikaci ne da ke aiki a cikin Abuja, amma yake zaune a Maraba, inda a kullum yake tasowa da sanyin safiya ya nufi Abuja, sannan ya koma bayan an tashi daga aiki.

A kullum Mu’azu ya fito, tunaninsa ina zai samu mai motar da zai rage masa hanya, idan kuma bai samu ba, haka yake shiga motar haya.

“Kafin a cire tallafin man fetur, kullum ina kashe akalla Naira 1,100 a kudin mota. Amma yanzu ina kashe akalla Naira 1,500 ne kudin mota a kullum.

“A bangaren abinci kuma, nakan kashe tsakanin Naira 1,000 zuwa 1,500 a kullum. Idan kuma wata ya ja, mutum sai ya hakura ya rika cin abincin dare kawai.”

Wannan matashi wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, ya ce kudin mota da abinci na cinye mafi yawan albashin da yake samu, inda da dan ragowar kuma ake hidimar gida da sauransu al’amuran yau da kullum.

Ba shi kadai ba ne, domin haka lamarin yake a wajen kusan duk ma’aikatan da suke aiki a Abuja da sauran jihohi bayan cire tallafin man fetur, wanda ya jawo hauhawar kudin sufuri a fadin kasar nan.

Aminiya ta ruwaito yadda cire tallafin, ya sa farashin man fetur ya yi sama, kuma ya jawo hauhawar farashin sufuri da kayan abinci.

Kamfanin NNPCL ne ya sanar da kara kudin man daga Naira 197 ya koma sama da Naira 500, inda har yake kai Naira 557 a wasu jihohi, wasu gidajen man ma har yakan kai Naira 700.

Da yake jawabi a kan kara farashin man lokacin da suke cire tallafin, Kakakin Kamfanin NNPCL, Garba Deen Muhammad ya ce sun yi haka ne kasancewar ya zama dole saboda yanayin kasuwa, inda ya ce gidajen mai mallakarsu za su rika sayar da man a tsakanin Naira 480 zuwa Naira 570.

Wannan lamari ya sa dole farashin sufuri da kayan abinci suka yi tashin gwauron zabo a Abuja da Legas da sauran birane.

Misali, daga yankin Lugbe da a da ake biyan Naira 200 zuwa Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Eriya 10, ya koma Naira 400.

Kudin mota daga Nyanya/Mararraba zuwa Berger da a da ake zuwa a Naira 250 zuwa 300, yanzu ya koma Naira 400 zuwa 500.

Daga Bwari zuwa Berger da Eriya 1 ya koma Naira 1,000 zuwa 1,200 maimakon Naira 500 da ake biya a baya.

Sannan daga Kubwa zuwa Berger ya koma Naira 800 zuwa 1,000 daga Naira 300 a baya.

“Yanzu ina so ne in samu in tara kudi, in kama gida a cikin gari kusa da inda nake zuwa aiki domin samun saukin wannan kudi da nake kashewa a mota. Yanzu rayuwar dole sai ana yi ana lissafi,” in ji Mu’azu.

A batun tafiya gida Kaduna kuwa, cewa ya yi, “A da na so a ce duk mako in je gida Kaduna, amma yanzu ba zai yiwu ba gaskiya. Kudin mota a tasha zuwa Kaduna Naira 5,000 ne.

“Ka ga zuwa da dawowa akalla Naira 10,000. Idan ka hada a wata ya zama Naira 40,000. Da wanne zan ji? Da kudin motar zuwa wajen aiki kullum ko na zuwa Kaduna duk mako?

“Zan so zuwa dai watakila duk mako biyu, ko uku ko kuma yadda yanayi ya kama kawai. Amma babu tabbas na in ce dole lokaci kaza zan rika zuwa gida.”

A Najeriya, mafi karancin albashi Naira 30,000 ne, wanda idan aka yi la’akari da tsadar rayuwa, za a iya cewa wasu ma’aikatan suna aikin ne ba riba.

A Abuja, karamin ma’aikaci yakan dauki albashin tsakanin Naira 40,000 zuwa 100,000.

Mu’azu da yake kashe kusan Naira 3,000 a kullum, zai kashe kusan Naira 60,000 a abinci da sufuri ke nan.

Tuni wasu ma’aikatu da kamfanoni suka fara yunkurin rage ranakun zuwa aiki domin rage radadin da ma’aikatan suke shiga na hannu-baka-hannukwarya.

A Jihar Legas ma haka abin yake, inda yawancin masu zuwa aiki suka koma tafiya a kafa maimakon hawa mota saboda tsadar kudin sufuri.

Daga yankin Oshodi zuwa Mil 2, wanda a da ake biyan Naira 400 ya koma Naira 800. Daga Agbarra zuwa Mil 2 kuma ya koma Naira 1,000 daga Naira 500 da sauransu.

A Jihar Kaduna, akwai ma’aikata da dama da suke zuwa aiki cikin garin Kaduna daga Zariya a kullum suna komawa.

Binciken Aminiya ya gano cewa yanzu kudin motar Zariya zuwa Kaduna ya koma Naira 1,500 maimakon Naira 700 a da, sannan daga tasha zuwa wajen aiki ma kudin ya karu sosai.

Haka Aminiya ta gano cewa ma’aikata da dama sun koma kwana a ofis, inda wasunsu suke komawa gida a karshen mako kawai kamar wadanda suke a wasu jihohi.

Wani ma’aikacin da ke zaune a Gwagwalada a Abuja tare da iyalansa, ya ce ba ya samun komawa gida sai a karshen mako, wani lokacin ma yakan yi mako biyu.

Shi ma wani ma’aikaci a daya daga cikin ma’aikatun mai suna Malam Shu’aibu ya ce kudin mota da yake biya don zuwa wurin aiki da komawa gida ya karu, inda ya ce a kullum sai ya kashe Naira 2,600 daga garin Suleja a Jihar Neja inda yake zaune da iyalansa.

“Ka ga nakan hau babur daga gidana wanda ba ya da nisa da Fadar Sarkin Suleja zuwa shatale-talen fadar a kan Naira 100, sannan in shiga motar Siyana a wajen zuwa shatale-talen Beger ko Kwanar Banex da ke cikin garin Abuja a kan Naira dubu daya.

Daga nan zan sake hawa tasi zuwa sakatariya inda ofishinmu yake a kan Naira 200, jimla ya kama Naira 1,300, a zuwa kadai,” in ji shi.

Ma’aikacin ya ce samun motar ofis na da wuya saboda da yawa daga cikin masu zuwa da motocinsu a yanzu sun koma suna bin motocin da ke karbar Naira 500 daga ofishinsu zuwa Suleja.

Ya ce haka akwai tsarin fifita ma’aikatan ofishi da ta mallaki mota kafin a dauki ’yan wasu ma’aikata daban.

“Misali motar Ma’aikatar Ilimi ko ta lafiya za su fifita daukar ma’aikatansu, idan aka samu rarar kujera ce za su dauki ma’aikacin da ba nasu ba.

“To cikin rashin sa’a babbar ma’aikatarmu ba ta da motar daukar ma’aikata da ke zuwa Suleja,” in ji shi.

Ma’aikacin ya ce wasu daga cikin masu motocin kansu da ke zuwa wurin aiki da su, na daukar ma’aikata ’yan uwansu a kan Naira dubu daya zuwa Suleja don rage kudin mai, wanda hakan ke matsayin rangwame, ga kuma fifiko na karamar mota a kan safa.

Ya ce sai dai duk da haka, su ma’akata da ke aiki a irin babbar sakatariyar na samun rangwamen kudin mota idan aka kamanta su da ma’aikatan da suke tasowa daga garin Suleja sannan su wuce wuraren aiki a yankuna kamar Apo ko Gudu da sauransu.

Ya ce haka lamarin yake ga masu aiki a wuraren da suke yankunan kasaita irin su Maitama ko Asokoro da yawanci sai dai shatar mota ce ke isa wajen.

A bangaren abinci kuwa, ma’aikacin ya ce kudin abincinsa na rana da a baya bai wuce Naira 700, yanzu ya koma Naira 1,200.

Hakan in ji shi a matakin kwarya-kwarya ne idan aka kamanta da na abincin rana na wasu a ma’aikatun da ke kashe kamar Naira 4,000 zuwa 5,000.

Ya ce a bangaren gida rayuwa ta yi tsada a dukkan matakan kula da iyali, lamarin da ya ce kudin albashinsa ba zai ishe shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here