Wasu ne za su cinye kudin rage radadin tallafin mai ba talakawa ba – Aliyu Ndume

0
114


Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun fara sukar shirin gwamnatin kasar na rage radadin janye tallafin man fetur.

Shirin wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi ya ciwo bashin dala miliyan 800 domin raba wa marassa galihu da sunan rage radadin cire tallafin mai.

Sanata Aliyu Ndume da ke wakiltar mazabar Borno ta kudu yana daya daga cikin ‘yan majalisar kasar da ke ganin kudin rage radadin ba za su kai ga marassa karfi ba.

Dan majalisar ya ce kudin sun yi kadan idan aka dubi yawan ‘yan Najeriya da ke fama da talauci.

“Yan Najeriya sama da miliyan 120 suna cikin talauci, ta yaya aka zabi mutum miliyan 50 da za a ba su tallafin kudin?” In ji Ndume.

Sanatan ya dora ayar tambaya kan yadda kudin za su amfani talakawa idan aka dubi yawansu da kuma yadda za a raba su.

“Rajistar da gwamnati ke cewa za ta yi amfani da ita wajen sanin talakawa ba ta gaskiya ba ce. Wannan dai wata hanya ce da suke so su fitar da ita don cutar da mutane,” a cewarsa.

Ndume ya ce bai ga hanyar da za a bi wajen zabo talakawa miliyan 50 daga cikin mutane sama da miliyan 200 da Najeriya ke da su ba cikin sauki.

“Idan ka yi lissafin adadin kudin wanda dala miliyan 800 ne da kuma yawan mutane da aka ce za a raba wa miliyan 50, kowane mutum bai fi ya samu Naira 11,840 ba”. in ji shi. 

Sanata Ndume ya kara da cewa komai talaucin mutum idon a ka bashi 11,840 ba wani taimako a ka yi masa ba saboda ko rabin buhun shinkafa kudin ba za su saya ba.

Dan majalisar ya bayar da shawara kan abin da ya kamata gwamnati ta yi da kudin domin su amfani talakawa a lungu da sakon Najeriya.

“Babban abin da ya kamata a yi amfani da kudin shi ne inganta kiwon lafiya a kananan hukumomi ta hanyar rarraba kudin ga kowace karamar hukuma, hakan zai sa kowacce ta samu kamar Naira miliyan 700 sai a sayi magunguna da kuma kayan aiki da kudin a zuba cikin asibitocin” a shawararsa.

Har’ilayau, ya ce za a iya amfani da kudin wajen gyara makarantu a kananan hukumomin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here