Kura ta turnike majalisar dattawa kan nadin shugaban marasa rinjaye

0
119

Kura ta turnike zauren majalisar dattawa kan gwagwarmayar neman mukamin shugaban marasa rinjaye.

Kurar ta turnike ne bayan da rikicin kujerar shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ya haifar da rashin jituwa a tsakanin sanatocin ‘yan jam’iyyar adawa na kokarin kaka ba musu shugabancin.

A majalisar dattawa ta 10, APC tana da sanatoci 59, PDP tana da 36, LP tana da 8, SDP na da 2, NNPP tana da 2, YPP na da 1, APGA na da 1.

Manyan mukamai hudu da aka ware wa jam’iyyun adawa a Majalisar Dattawa su ne, shugaban marasa rinjaye, mataimakin shugaban marasa rinjaye, mai tsawatarwa na marasa rinjaye da mataimakin mai tsawatarwa.

A wani yunkuri na samun hadil kai abokansa a matsayin shugaban marasa rinjaye a zauren majalisar dattawa, tsohon gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a ranar Alhamis da ta gabata.

Ganawar ya gudana ne a zauren majalisar na tsawan awanni da dama. Wike ya bar majalisar ne da misalin karfe 6:30 na yamma ba tare da ya yi magana da manema labarai ba.

An ce tsohon gwamnan Jihar Ribas ya bukaci abokinsa, Kingsley Chinda a matsayin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da shi ba.

Sai dai PDP da ke da kujeru mafi rinjaye a ‘yan majalisar dattawa 36 daga cikin jam’iyyun adawa, ta sha alwashin yin tir da duk wani makirci da jam’iyyar APC mai mulki ko wasu masu ruwa da tsaki za su yi na kulla alaka da ‘yan tsiraru a majalisar dattawa domin nada shugaban marasa rinjaye.

Har ila yau, ‘yan majalisar daga bangaren ‘yan adawar sun ce suna sane da matakin kutse a ciki da wajen majalisar dattawa ake yi na raba kan ‘yan tsirarun jam’iyyu da kuma samar musu da shugabancin da bai dace ba. Duk da haka, sun ba da tabbacin cewa makircin ba zai yi tasiri ba.

Da yake zantawa da Jaridar Daily Trust a jiya, Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce ‘yan Nijeriya sun tabbatar da cewa jam’iyyar PDP tare da sanatocinta za su kafa wasu tsirarun shugabannin da za su tabbatar da raba madafun iko da kuma tantancewa.

Ya ce, “Jam’iyyarmu jam’iyya ce take da tsari kuma muna bin ka’idojinmu. A kan batun shugabancin marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, PDP na tuntubar sanatocinta bisa tsarin dimokuradiyyarmu.

“Abin da ya fi dacewa a gare mu a jam’iyya shi ne, samun shugabancin masara rinjaye da zai tabbatar da tsayayyen adawa a majalisar dattawa da kuma maslahar ‘yan Nijeriya baki daya.

“Za mu mai da hankali kan tabbatar da cewa an bi tsarin dimokuradiyya da kuma ka’idojin raba madafun iko. Muna tuntubar jama’armu kuma bayaninsu ya yi daidai da matsayinmu na jam’iyya, muna tattaunawa da su, kuma a karshe za mu fitar da matsayinmu na samun tsayuwar adawa mai karfi a cikin majalisar kasa.

“Za mu tabbatar an bi ka’idojin tsarin mulki,” in ji shi.

Tun a ranar Asabar da ta gabata, ‘yan majalisar dattawa daga jam’iyyun adawa sun sha alwashin yin fatali da duk wani yunkuri na dora musu shugaban marasa rinjaye wanda bai dace ba a zauren majalisar dattawa.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa na ‘yan majalisar da suka fitar sun ce ‘yan adawa za su zabi shugabanninsu ne bayan tattaunawa da jam’iyyun siyasarsu ba tare da tsangwama daga masu yin kutse ga tsarin dimokuradiyya ba.

Sun jadadda cewa har yanzu babu wani sanata da aka amince da shi ko aka zaba a matsayin shugaban marasa rinjaye.

Sanarwar ta samu sa hannun hadin gwiwar Mohammed Adamu Aliero, Henry Seriake Dickson, Aminu Waziri Tambuwal, Abdul Ningi, Patrick Abba Moro, Ezenwa Francis Onyewuchi, Sumaila Kawu da kuma Ifeanyi Patrick Ubah.

Ta ci gaba da cewa, “Ga zuwa yanzu dai, ‘yan jam’iyyun adawa a zauren Majalisar Dattawan ana kokarin raba kan ‘yan adawa kuma yi musu zagon-kasa wajen kakaba musu shugabanni.

“Mun yi alkawarin yin aiki tare da sabbin shugabannin majalisar dattawa da bangaren zartarwa don isar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Nijeriya. Don haka muna ba da shawara da lura cewa ka da su taimaka wa wata kungiya a ciki ko wajen majalisar dattawa don raba kan ‘yan adawa.

“Sanatocin jam’iyyun adawa za su gana idan majalisar dattawa ta dawo daga hutu, kuma za mu tuntubi jam’iyyun siyasarmu wajen zaben shugabanninmu ba tare da tsangwama daga masu kutse a dimokuradiyya a ciki ko wajen majalisar dattawa ba.

“Don kauce wa shakku, har yanzu babu wani sanata da aka amince da shi ko aka zaba a matsayin shugaban marasa rinjaye saboda bin tsarin da ya dace kamar yadda dukkanin ‘yan dawa suka amince a taronsu na karshe.

“Ba za lamunci duk wani yunkurin kafa mulkin kama-karya na jam’iyya mai mulki ba.
“Muna kira ga dukkan ‘yan jam’iyyun siyasa marasa rinjaye da su yi aiki tare cikin hadin kai don kare tsarin dimokuradiyya na majalisar dattawa da na Nijeriya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here