Dangote ya tallafa wa ‘yan Najeriya da suka dawo daga Sudan

0
133
Dangote
Dangote

Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da tallafi ga wasu ‘yan Najeriya da yaƙin Sudan ya tilasta musu komawa ƙasar.

Mutane 125 da suka koma Najeriya ranar Asabar da ta gabata suka haɗar da gajiyayyu, kowannensu ya samu tallafin naira 100,000 da wasu kayyakin ihsani a cikin jaka, daga gidauniyar ta Dangote.

A cikin watan Mayu fiye da mutum 2,278 suka samu tallafin 100,000 kowannensu da abubuwan ihsani domin samun saukin haɗuwa da iyalansu, bayan dawo da su ƙasar daga Sudan.

Daga cikin mutanen da aka kwaso cikin makon da ya gabata har da wasu tsofaffi biyu da suka yi shirin zuwa Umara a mota, hanya ta bi da su ta birnin Khartoum, suka kuma faɗa tarkon yaƙin da ake gwambazawa a birnin, lamarin da ya sa suka rasa duka guzurinsu.

Wani dattijo mai suna Muhammad Saidu Ahmed ya ce ”Na dawo daga Sudan ba tare da ko sisi ba, amma yanzu na samu 100,000”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here