Yadda rusau ke ƙara jefa mutane cikin fargaba a Kano

0
215
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Wasu masu gine-gine a jihar Kano na ci gaba da bayyana halin da suke ciki na fargaba, sakamakon yiwuwar rushe musu gini daga nan zuwa kowanne lokaci.

Masu irn wadannan gidaje sun ce tuni an shafa masu jan fentin gargadi, wata alama da ke nuna cewa daga nan zuwa kowanne lokaci za a iya zuwa a rushe musu gidajen nasu.

Wani magidanci a unguwar Salanta ya bukaci gwamnatin ta duba wannan al’amari duba da halin da suka tsinci kansu.

A cewarsa ”Ni ba dan siyasa ba ne, kuma ‘yan unguwar nan gwamnati suka zaba, an bi mu kasuwa yanzu an biyo mu gida za a hana mu barci, ya kamata a duba wannan al’amari, mun bi ka’ida amma ana son a fitar da mu daga gidajenmu”.

Alhaji Abubakar Zakari Muhammad wani da ya garzaya kotu don kalubalantar shirin rushe gidansa bayan an shafa masa jan fenti, ya ce yanzu haka magana na gaban kotu, kuma tuni an ba wa hukumar tsara birane ta jihar umarnin dakatawa har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.

Suma a nasu bangaren ƴan kasuwa da lamarin ya shafa na ci gaba da kokawa kan irin asarar da rusau ɗin ya janyo musu.

Alhaji Sharif Nata’ala Isma’il, shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin ƴan kasuwa na kasuwar Kofar Wambai, kuma ya shaida wa BBC cewa sun yi asarar da ta kai ta Naira Biliyan guda.

”Yanzu haka a kasuwa muke kwana, don kowanne lokaci za a iya shigowa a mana abun da ba shi kenan ba, a razane muke, a matsayin gwamnati na uwa ya kamata ta tausaya mana” in ji shi.

Me gwamnatin ke cewa ?

Rusau din ya janyo ce-ce-ku-ce

Ita dai gwamnatin jihar Kanon karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf, na zargin cewa an yi gine-ginen ne ba bisa ka’ida ba, a filayen al’umma, don haka take kokarin kwacewa don mayar da su ga jama’ar Kano.

A cewar sakataren gwamnatin jihar Dr Abdullahi Baffa Bichi, ba wai rusau ake yi ba, gyara ake yi.

”Lallai-lallai ya kamata al’umma su yarda cewa wuraren da aka ware a matsayin makarantu, ko asibitoci, ko makabartu ba wurare ne da wani zai zo ya yanka don yana da wani mukamin gwamanti ya sayar ba”. in ji shi.

Ya kara da cewa ”Babu yadda za a ce kana gani a tsaga makaranta a sayar maka, ga dakin karatu ga azuzuwan yara amma ka saya ka gina gida, wannan abu ne da ya saba ka’ida, don haka abin da muke kokarin yi shi ne mu karbe mu dawowa da mutanen Kano kayansu”.

”Akwai asibitin fa da gidajen likitoci aka rushe aka gina gidan biki, akwai makarantar da aka kori dalibai aka sayar da makarantar, aka mayar da su kauye, yanzu fisabilillah da ace gwamnonin da suka gabata haka suka yi shi ina zai samu inda zai sayar?” in ji Dr Baffa.

Tun dai kafin a rantsar da shi a matsayin gwamna ne, gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf ke gargadi ga masu gine-gine a filayen gwamnati a jihar su daina.

Kana ya yi yakin neman zabe da alkawarin idan ya samu nasara, zai kwace filayen da jam’iyyarsu ta NNPP ke zargin gwamnatin Ganduje da ta gabata ta sayar wa makusantanta ba bisa ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here