Chelsea ta cefanar da Mount zuwa Man United

0
187
Mason Mount
Mason Mount

Manchester United ta kulla yarjejeniya da Chelsea kan sayen Mason Mount kan kudi fam miliyan 60.

Yarjejeniyar ta hada da yuwuwar fam 5m na abubuwan da suka dogara da karfi kan bayyanar da nasara. United ta yiwa dan wasan na Ingila tayin kwantiragi na shekaru biyar tare da wani zabin karin shekara.

Mount yana da shekara guda a kwantaraginsa a Chelsea kuma an fahimci yana son komawa kungiyar Man United karkashin Erik ten Hag.

Chelsea tayi watsi da tayi uku da United din tayi akan Mount, amma kara komawa kan tayin a baya bayan nan an samu nasarar cinikin inda yanzu an amince da tayin.

Yanzu haka Mount zai tafi Manchester domin duba lafiyarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here