Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya zai habbaka a bana

0
139

Bankin Duniya ya ce Najeriya za ta iya alkinta kudin da yawansu ya kai Naira tiriliyan 3 da biliyan 900 a shekarar bana kadai, sakamakon garambawul din da gwamnatin kasar ta yi wa tsarin tattalin arzikinta, matakin da ya shafi canjin kudaden kasashen ketare da kuma soke shirin tallafin man fetur. 

Babban jami’in da ke wakiltar bankin duniya a Najeriya Alex Sienaert ne ya yi wannan hasashe yayin gabatar da wata mukala kan lamurran tattalin arziki a birnin Abuja. 

Hasashen bankin duniyar ya ce yana sa ran karuwar karfin tattalin arzikin Najeriya da kashi 3.3 a bana, yayin da sai kuma a shekarar badi ta 2024 da ake sa ran tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 3.7. 

Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa ne da, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da soke biyan kudaden tallafin man fetur, shirin da kididdiga ta nuna cewar a shekarar bara kadai sai da ya lakume wa gwamnati dala biliyan 10. Makwanni kadan bayan cire tallafin man ne kuma, gwamnatin ta Tinubu ta mayar da tsarin canjin kudaden kasashen ketare zuwa na bai daya, abinda  ya sanya darajar dalar Amurka guda haura naira 700. 

Sai dai a yayin da bankin duniyar ya yaba da matakan da Najeriya ta dauka, yayi gargadin cewar al’ummmar kasar za su fama da hauhawar farashin kayayyaki, kalubalen da y ace na takaitaccen lokaci ne, domin al’amura za su daidaita zuwa nan gaba. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here