Tinubu ya sanya wa filin jirgin saman Maiduguri suna Muhammu Buhari

0
211

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta canza wa wasu filaye 15 zuwa sunan wasu fitattun ’yan Najeriya.

Daga cikin sunayen har da filin jirgin sama na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, wanda aka saka wa sunan tsohon Shuagaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Umarnin dai na kunshe a cikin wata wasika da aka aike wa dukkan Shugabannin Gudanarwa na filayen jiragen, wacce ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta aike mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Yunin 2023.

Wasikar na dauke ne da sa hannun Daraktar Kula da Filayen a Ma’aikatar, Misis Joke Olatunji.

Ga cikakkun filayen da sunayen wadanda aka sanya musu

  1. Filin jirgin sama na Akure – Olumuyiwa Bernard Aliu
  2. Filin jirgin sama na Benin – Oba Akenzua II
  3. Filin jirgin sama naDutse – Muhammad Nuhu Sanusi
  4. Filin jirgin sama naEbonyi – Chuba Okadigbo
  5. Filin jirgin sama naGombe – Birgediya Zakari Maimalari
  6. Filin jirgin sama naIbadan – Samuel Ladoke Akintola
  7. Filin jirgin sama naIlorin – Janar Tunde Idiagbon
  8. Filin jirgin sama naKaduna – Hassan Usman Katsina
  9. Filin jirgin sama naMaiduguri – Janar Mumammadu Buhari
  10. Filin jirgin sama naMakurdi – Joseph Sarwuan Tarka
  11. Filin jirgin sama naMinna – Mallam Abubakar Imam
  12. Filin jirgin sama naNassarawa – Sheikh Usmanu Dan Fodio
  13. Filin jirgin sama naOsubi – Alfred Diete Spiff
  14. Filin jirgin sama naFatakwal – Obafemi Awolowo
  15. Filin jirgin sama naYola – Lamido Aliyu Mustapha

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here