Najeriya ta rasa Mahajjata biyar a Saudiya

0
166

Hukumar kulada aikin Hajji ta Najeriya, ta tabbatar da mutuwar alhazanta biyar a kasar Saudiya a lokacin aikin Hajjin bana.

Shugaban bangaren kulada lafiyar hukumar Usaman Galadima ne ya bayyana haka, a lokacin taron da hukumar ta gudanar a birnin Makkah, inda ya ce yanzu haka akwai wasu mutum 30 da ke fama da rashin lafiyar kwakwalwa.

Ya ce jahohin Osun da Kaduna ke da mahajjata biyu-biyu da suka rasu, ya yinda jahar Filato ke da mahajjaci daya.

Galadima ya ce marasa lafiyar na samun kulawar da ta kamata a cibiyar kulada lafiya ta kasar, kuma ana saran za su gudanar da aikin Hajji.

Har wayau, Galadima ya ce mahajjata mata biyu sun yi bari, sannan kuma wata mahajjaciyar Najeriya ta haihu a aikin hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here