Tsuntsaye jan-baki sun lalata gonakin shinkafa kusan 100 a jihar Kebbi

0
184

Aƙalla mutum 100 ne suka rasa gonakinsu yayin da dandazon tsuntsaye jan-baki suka afka wa gonakin shinkafa a garin Argungu na jihar Kebbi.

Mazauna yankin sun ce tsuntsayen sun lalata kusan hekta 75,000 na gonankin a ranakun ƙarshen makon nan.

“Bayan matsalolin da muke ciki na tsadar man fetur da taki, ga kuma tsuntsaye. Mutum bai isa ya zauna a gida ba, in ba haka ba kuma za su lalata gonarsa baki ɗayanta,” a cewar wani manomin shinkafa Malam Adamu.

Wani manomin mai suna Garba Umar ya ce ya shafe shekara 20 yana noman shinkafa amma bai taɓa ganin irin wannan bala’i ba.

Ba wannan ne karon farko da ake samun hare-haren tsuntsayen ba amma wannan ne mafi muni a baya-bayan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here