Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun ja kunnen gwamnati kan shirin karin kudin lantarki

0
149

Gamayyar kungiyoyin Kwadagon Najeriya da ta ‘yan kasuwa da ta farar hula sun yi watsi da shirin karin kashi 40 na kudin wutar lantarki, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, inda suka yi kira ga gwamnati da ta yi watsi da karin kudin.

Kungiyar NLC ta bayyana shirin kara kudin lantarkin amtsayin rashin sanin ya kamata yayin da TUC kuwa ta bayyana shirin amatsayin kololuwar rashin kula da halin da talakawan kasar ke ciki.

A nasu bangaren, kungiyoyin farar hula ta CSO sun bukaci gwamnati da ta gaggauta janye shirin da suka bayyana a matsayin rashin adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here