Bousquets ya koma Inter Miami bayan barin Barcelona

0
165

Bousquet, tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona ya cimma yarjejeniyar da zuwa Inter Miami ta Amurka bayan shafe shekaru 14 a tsohuwar kungiyarsa da ya kasance kyaftin a shekarunsa na karshe a kungiyar.

Bousquet wanda ake ganin yana daga cikin ‘yan wasan da suka fi iya wasan tsakiya a tarihin kwallon kafa ya yanke shawarar barin Fc Barcelona a karshen kakar bana inda ya shafe tsawon rayuwar kwallonsa tun yana matashi.

A tsawon zaman da ya yi a kungiyar ya buga wasanni sama da 700 ya jefa kwallaye 11 sannan kuma ya lashe kofuna 32 wadanda suka hada da Uefa Champions League 3, Spanish Laliga 9 da sauransu.

Bayan barin kungiyar, Bousquet na neman samun wata sabuwar kungiya da kuma sabuwar rayuwa inda kungiyoyi da dama daga yankin larabawa suka neme shi. Bousquet ya lashe gasar kofin Duniya tare da Spain a shekarar 2010 da aka buga a kasar Afirika ta Kudu.

Amma Bousquet ya zabi ya tafi zuwa Inter Miami ta kasar Amurka domin sake haduwa da tsohon abokin kwallonsa kuma amininsa Lionel Messi wanda ya koma can daga PSG.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here