Hukuncin Talbiyya da falalar tsayuwar Arfa

0
164

Ma’anar Talbiyya ita ce yin “Labbaikallahumma labbaik, Labbaika la shariyka laka labbaik, innal-hamda wanni’imata laka wal-mulk, la shariyka lak.” Kamar dai yadda idan an ce Hailala, ana nufin “La ilaha illalal Lah”.

Dukkan Malamai sun hadu a kan cewa an shar’anta yin Talbiyya da zarar mutum ya yi harama da Hajji. Galibi an dauke ta a matsayin wajiba a Maz’habar Malikiyya. Idan mutum ya bar ta ko bai hada ta da yin haramar Hajji ba (lokacin niyya) ko ya jinkirta ta, to sai ya ba da jini.

Lafazinta kamar yadda Annabi (SAW) ya yi wanda Imam Malik ya ruwaito daga Nafi’u, shi kuma ya ruwaito daga Abdullahi bin Umar (RA), shi ne “Labbaikallahumma labbaik, Labbaika la shariyka laka labbaik, innal-hamda wanni’imata laka wal-mulk, la shariyka lak.”

Fassarar ta ita ce “Amsawa gare ka ya Allah, ya Ubangiji na amsa maka, babu wani abokin tarayya gare ka ya Allah, na amsa maka, godiya da ni’ima da mulki duk gare ka suke, babu wani abokin tarayya a gare ka”.

Malamai sun so a tsaya a kan wannan lafazin, saboda shi ne aka ji daga Annabi (SAW). Amma sun yi sabani a kan kara wani abu a kan haka, koda yake; galibinsu sun ce babu laifi. Saboda Sayyidina Umar (RA) ya kara, shi ma Sayyidina Abdullahi bin Umar (RA) da ya ruwaito wannan din ma ya kara.

Talbiyya tana da falala mai yawan gaske. Ibn Majah ya ruwaito Hadisi daga Jabir bin Abdullahi (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce “Babu wani da zai yi harama da Hajji, yana mai yin Talbiyya har zuwa faduwar rana, face ranar ta fadi tare da zunubinsa (zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi)”.

Abu Huraira (RA) ya ce Annabi (SAW) ya fadi cewa “Idan mai niyyar Hajji ya daga murya da Talbiyya, za a yi ma sa bishara. Shi ma mai kabbara yayin zaman Mina, ba zai yi hakan ba face an ma sa bishara.” Sai aka tambaye shi (SAW) cewa “ya Rasulallahi bisharar ta Aljanna ce?”, ya amsa da “Na’am”. Dabarani ya fitar da wannan Hadisin da Sa’adu bin Mansurin.

Haka nan, an karbo daga Sahli bin Sa’adin cewa Manzon Allah (SAW) ya ce “Babu wani Musulmi da zai yi Talbiyya face – duk – abin da yake damansa da hagunsa ya amsa ma sa.” Ibn Majah da Baihaki suka ruwaito, Hakim ya inganta Hadisin. Ma’ana ko wane abu da ke damansa har karshen duniya zai amsa ma sa, haka nan abin da ke hagunsa. To wa ya san adadin abubuwan da za su amsa wa mutum? Kuma duk ladan (amsawar halittun) nasa ne ba na wani ba.

•Daga murya wajen yin Talbiyya

An fi so a yi Talbiyya a bayyane ba a boye ba. Ana so mutum ya daga murya (ba can da karfi ba) wurin yin ta.

Hadisi ya zo daga Zaidu bin Khalid cewa, Annabi (SAW) ya ce, “Jibrilu (AS) ya zo mun, sai ya ce “Ka hori Sahabbanka su daga muryarsu wajen yin Talbiyya. Ita tana daga cikin alamomin Aikin Hajji.” Ibn Majah, Ahmad, Ibn Khuzaima da Hakim suka ruwaito. Hakim ya ce danganen Hadisin ingantacce ne.

An karbo Hadisi daga Sayyidina Abubakar (RA) – Hadisinsa gwal ne – cewa, an tambayi Manzon Allah (SAW) shin wadanne ayyuka ne a cikin ayyukan Hajji suka fi falala? Sai ya amsa da cewa, “Daga murya wajen yin Talbiyya da Kabbarorin da ake yi (na Jifa da zaman Minna), sai zubar da jini (Hadaya).”

Annabi (SAW) rakuma 100 ya yanka don ya nuna wa al’umma falalar zubar da jini a Aikin Hajji. Idan aka buga lissafin kudin rakuman a yanzu za a ga cewa milyoyi ne. Ya kamata wadanda suke da hali su yi kokarin koyi.

Wadanda ba su da shi kuma su yi bakin gwargwado, amma kar mutum ya kasance yana da halin yi kuma ya ki yi, wannan babu kyau. Don haka a kiyaye. Allah kuma ya hore ga duk Musulmi kowa ya yi.

Hadisi ya zo daga Ibn Hazim cewa, “Sahabban Manzon Allah (SAW) sun kasance idan suka yi harama da Hajji, kafin su iso Rauha’a daga Zhul-hulaifa (babu nisa sosai) muryoyinsu kan shake – saboda daga murya wurin yin Talbiyya.”

Malamai da dama sun so a daga murya wurin yin Talbiyya. Sai dai, Imam Malik (RA) ya ce “kar dai mutum ya daga murya a cikin Masallatai don gudun hana mutane – karatu – a cikin sallah.” Don haka sai mutum ya jiyar da kansa kawai. Amma a Masallaci Mina, za a iya dagawa. Haka nan Ka’aba, kafin mutum ya fara Dawafi da Safa da Marwa.

Duk wannan daga murya da ake bayani a kai, ana nufin maza ne banda mata. Ita mace kanta za ta jiyar kawai ba a so ta daga murya, kamar yadda Malam Ada’u ya yi bayani.

Wuraren da ake so a daga Murya

Da yake aikin Hajji ba na lokaci daya ba ne, dole akwai wuraren da za a ji cewa an gaji da daga muryar. Don haka sai aka kebence wasu wurare da aka fi so a daga murya a can.

Yana daga ciki an fi so a daga murya da Talbiyya idan an hau abin hawa bayan an yi harama. Kamar misali, idan an hau mota ko kuma bayan an tsaya a wani wuri aka ci abinci, to da an dawo cikin motar sai a cigaba da daga muryar. Haka nan idan an sauka.

Koda an yi shiru yayin da ake kan abin hawa, idan an zo shigewa ta wani dutse ko tudu ko gangare ko korama, nan ma ana so a daga murya da Talbiyya.

Haka nan idan an hadu da wata tawaga ta alhazai. Da gurbin ko wace sallar farilla bayan kammalawa. Imamu Shafi’i (RA) ya ce “mu muna son ta (daga murya da Talbiyya) a ko wane hali.”

Lokacin fara Talbiyya da kammalawa

Imam Malak (RA) ya ce idan mai harama ya yi harama da Hajji ko Umura ko duka, zai fara Talbiyya tun daga nan har zuwa lokacin da zai sumbanci Hajrul As’wad da nufin fara Dawafi.

Idan Umura ce kawai mutum zai yi, da zarar ya yi saisaye shikenan. Idan kuma Hajji ne, ga mai yin Hajjin Tamattu’i zai fara daga ranar 8 ga wata, ba zai daina ba har sai an sauko daga Arfa. Ana so bayan mutum ya yanke yin Talbiyyar, sai ya yi Salati ga Manzon Allah (SAW) da sauran addu’o’i. Saboda nan wajen karbar addu’a ne. Wannan ita ce fahimtar mafi akasarin Malamai.

Garabasa da falalar tsayuwar Arfa

Idan aka ce Tsayuwar Arfa, ba ana nufin mutum ya yi ta tsayawa ne kyam, babu zama, babu hutawa, babu kwanciya ba, a’a, ko mutum barci yake yi a filin Arfa to yana daga cikin tsayuwar Arfan.

An karbo Hadisi daga Jabir (RA) Annabi (SAW) ya ce “Babu wasu kwanaki masu daraja da girma a wajen Allah da suka fi kwana goma nan na farkon watan Sallar Layya”.

A cikin kwanakin ne ake hawa Arfa a ranar 9 ga wata, ranar 10 ga wata ake gudanar da sauran manyan ayyukan Hajji irin su Jifa, Hadaya, Aski da Dawaful Ifada. Kuma a rannan ne sauran Musulmi a duk inda suke a duniya suke yin Sallar Idi da taya Alhazai yanka da liyafar taya su murnar sun yi Hajji lafiya.

Wasu Malamai sun yi bayanin cewa hatta kwana 10 na karshen watan Ramadan ba su kai wadannan kwanaki goman ba. Shi ya sa yin azumi a cikinsu ga wanda ba ya Aikin Hajji, da yin nafilfilin dare suke da dimbin falala.

Wani mutum ya tambayi Annabi (SAW) cewa “Kwana 10 din nan sun fi hatta yakin tsayar da Tafarkin Allah da ake cewa wanda ya mutu a ciki Dan Aljanna ne, wanda ya dawo – da rai – zai dawo da lada mai yawa?”. Annabi (SAW) ya ce “Eh, sun fi yakin tsayar da Tafarkin Allah.”

Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren wadannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”. Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a huldar da ke tsakaninmu ba.

Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a rika fassarawa da yadda kananan kwakwalenmu ke daukawa ba. Duk wanda ya ce zai fassara da karamin hankalinsa, to wannan ya sa wasa a cikin sha’anin Allah (SWT).

Hadisin ya ci gaba da cewa “Ubangiji yana sauka a saman duniya sai ya yi alfahari da mutanen doron kasa. Yana kallon mutanen yana wa Mala’iku alfahari da su cewa ku kalli bayina, sun zo mun da birkitaccen gashi masu kura-kura, ga su sun yini, sun zo mun daga nesan duniya suna neman rahamata, ba su ga azabata ba.” Munzir ya ce Abu Ya’ala, Bazzaru, Ibn Khuzaima da Ibn Hibban suka ruwaito Hadisin. Amma lafazin da aka ruwaito da shi kuwa, na Ibn Mubarak ne daga Safyanus Sauri, shi kuma daga Zubairu bin Aliyin daga Anas bin Malik (RA).

Ma’anar kai ya yi kura-kura, ko da gashin mutum bai yi kura ba, Allah zai ba shi ladan, shi dai ya kasance ya kiyaye abubuwan da Shari’a ta ce ma sa kar ya yi. A kan haka ne ya sa ba a so a rika yin kwalliya bayan wanda aka yi a yayin daukan harami.

Annabi (SAW) ya ce ba a taba ganin wata ranar da ake ‘yantar da bayi daga barin shiga wuta kamar Ranar Arfa ba. Duk zunubin da aka yi a shekara, rannan Allah yana zubar da shi.

An karbo kuma daga Ibn Mubarak, daga Safyanus Sauri, daga Zubairu bin Aliyin, shi kuma daga Anas bin Malik (RA) ya ce, “Annabi (SAW) ya tsaya a Arfa, da rana ta kusa faduwa, sai Annabi ya kira Bilalu ya ce ya sa mutane su yi shiru zai yi magana, sai Bilalu ya tashi ya ce wa jama’a; ku yi shiru ga Annabi (SAW). Sai Annabi (SAW) ya tashi yana kan rakumi ya ce, “Ya ku taron mutane, yanzu Jibrilu ya zo mun ya gaishe ni, ya ce Ubangijina ya gafarta wa duk wadanda suka zo Arfa din nan, da wadanda duk suka zo Mina (Mash’aril Harami) kuma Allah ya lamunce musu duk laifin da ke kansu”. Sai Sayyidina Umar bin Khaddab (RA) ya mike ya ce “Ya Ma’aikin Allah, wannan namu ne da muka zo wannan Hajjin kawai? Sai Annabi (SAW) ya amsa ma sa da cewa “Naku ne kuma da duk wadanda za su zo Arfa a bayanku har tashin Kiyama”. Sai Sayyidina Umar (RA) ya ce “Alherin Allah yana da yawa kuma ya yi dadi”. Imam Muslim da waninsa suka ruwaito.

Har ila yau, an karbo wani Hadisin daga Ummul Mu’umina Aisha (RA) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Babu wata rana da Allah yake yawaita ‘yanta bayinsa daga wuta kamar Ranar Arfa. Ubangiji yana kusantowa (SWT) ga mutane har ya yi wa Mala’iku alfahari da su ya ce, “Me wadannan mutane suke so ne?”.

Wannan yana nuna tambayar ta jindadi ce (yadda ya dace da Allah), saboda ai ya san abin da kowa yake so amma kuma sai ga shi (SWT) yana tambayar Mala’iku. Hakika ba karamar falala ba ce a ce Allah ya yi alfahari da mutum, Alhamdu Lillah.

An karbo Hadisi daga Abu Darda’i (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Babu wata rana da ake ganin Shaidan a matsayin mafi kaskanci da wulakanta da tunkudewa da fushi kamar Ranar Arfa”. Ba komai ya jawo ma sa wannan ba sai abin da yake gani na Rahamar Allah da take sauka.

Hatta shi kansa Shaidan yana zuwa Arfa, a maimakon shi ma ya samu yafiya a wurin Allah, sai kuma ya sake jibgan wani laifin saboda hassada a kan Rahamar da Allah yake wa bayinsa. Yana-ji-yana-gani, Allah zai yafe wa al’umma duk sabon da ya ingiza su suka aikata.

Wannan bakin cikin ma bai isa ba, tun da har ya yi hassada, ya ji bakin cikin gafarar da Allah ya yi wa bayinsa, za a kuma tafi Mina bayan an sauko daga Arfa a jefe shi a can.

Ko kuma dama shi duk mai hassada idan ya ga wanda Allah ya baiwa ni’imar da yake bakin ciki a kai; sai ya ji rashin lafiya ta taso ma sa. Abin da yake samun Iblis kenan. Al’umma za su taso daga Arfa cikin gafara kuma su je su jefe shi.

Haka nan, ya yi irin wannan bakin cikin Ranar Badar. Da aka tambayi Annabi (SAW) irin bakin cikin da ya yi a ranar, Annabi (SAW) ya ce “Iblis da ya ga Jibrilu yana jagorantar Rundunar Mala’iku, ba a taba ganin tsoro ya kama shi irin na rannan ba, har ma ya mance ya ce yana tsoron Allah”.

Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu dora insha Allahu da batun hukuncin Arfa a rukunin Aikin Hajji.

Allah ya amfanar da mu baki daya, Albarkar Annabi (SAW).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here