Karya darajar Naira: Farashin ragon Layya ya ninka bara

0
178

Farashin dabbobin layya ya nunka na bara a faɗin Najeriya sakamakon tashin farashin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.

Tashin farashin litar mai daga N195 zuwa N540 ko fiye da haka ya jawo ƙaruwar kuɗin sufuri.

Masu shigo da dabbobin daga ƙasashen maƙwabta kuma na fama da karyewar darajar Naira wacce ta faɗo zuwa N770/$1 a kasuwar canji.

Wakilanmu sun tattaro muku farashin ragon na bana daga Abuja, Lagos, Kano da Ilorin.

Wakilinmu da ya kewaya kasuwanni dabbobi a Abuja ya tarar cewa a Kasuwar Jabi farashin rago ya fara ne daga N180,000 har zuwa N700,000.

A karar Kubwa, farashin rago ya kama daga N60,000 zuwa N320,000.

Daga Legas kuwa, wakilinmu ya gano cewa  ragunan da a bara ake sayar da kamarsu N50,000 sun koma N120,000.

A Kasuwar Kara dake titin Lagos-Ibadan ana sai da matsaikacin rago N100,000.

Farashin da dama-dama a  Ilorin  inda ake samun ragon layya daga N55,000 zuwa N400,000.

Amma ragunan sun fi sauƙi a Kano inda a  Kasuwar Ƴan Awaki, ake samu daga N30,000 zuwa N270,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here