Har yanzu ba a gano attajiran da suka bace yayin yawon bude ido a karkashin teku ba

0
144

Jami’an ceto masu linkaya sun dukufa wajen kokarin gano wasu masu yawon bude ido da suka yi batan dabo akan hanyarsu ta yin nutso zuwa karkashin tekun Atlantic 3, domin isa ga ragowar tarikicen katafaren jirgin nan na Titanic da yayi hatsari a shekarar 1912

Jami’ai sun ce tun tun a ranar Lahadi suka daina musayar sako da jirgin nutson masu yawon buden idon da suka hada da hamshakin attajirin Birtaniya Hamish Harding da takwaransa na Pakistan Shahzada Dawood da kuma dansa Suleman.

Sauran mutanen da ke cikin jirgin da ya bace sun hada da Paul Henry Nargeolet wani fitaccen mai linkaya da kuma shugaban kamfanin safarar jiragen ruwa masu nutso zuwa karkashin teku na OceanGate wato Stockton Rush.

Bayanai sun ce jirgin ruwan ya buga nutso ne da zummar yin tafiyar kilomita 3 da kusan rabi, jigilar da ba ita ce karo na farko da jirgin da ake kira da Titan ke yin irinta ba, domin kuwa ya fara ne tun daga shekarar 2021.

A halin yanzu jami’an tsaron gabar teku na Amurka ne ke jagorantar neman karamin jirgin nutson zuwa karkashin teku na Titan, a yankin da ke arewacin Tekun Atlantic mai nisa, inda jirgin ruwan Titanic mai tarihi ya bugi wani dutsen kankara, hatsarin da ya haddasa nutsewar zuwa karkashin tekun, tare da hasarar rayukan fasinjoji kusan 2,200 daga cikin akalla dubu 3,100 da ke cikin jirgin a 1912

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here