Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya maka gwamnatin tarayya a kotu

0
142

Gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Mista Godwin Emefiele ya shigar da ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya, yana ƙalubalantar tsare shi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ke yi.

A cikin ƙudurin da ya gabatar, Emefiele ya nemi kotu ta tilasta wa hukumomi tabbatar masa da ‘yancinsa na walwala da ‘yancin zirga-zirga, don kuwa a cewarsa, babu hujjar ci gaba da tsare shi.

Sai dai, Ofishin Atoni Janar na Tarayya da kuma hukumar DSS sun ce tsare dakataccen gwamnan bankin yana kan doka.

Sun kuma ce tsare jami’in ya dogara ne kan wani umarnin kotun majistare don haka suka nemi babbar kotun ta kori buƙatar da Emefiele ya gabatar.

Sun nunar da cewa kama tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya yana kan tsarin gudanarwa na hukumar ta DSS.

Yayin da Atoni Janar na Tarayya ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraron ƙarar, saboda ƙudurin da Godwin Emefiele ya gabatar na neman kotu ta jingine umarnin tsare shi ne, maimakon neman a tabbatar masa da ‘yancinsa.

Haka zalika, ita ma hukumar DSS a nata ɓangare ta ƙalubalanci ƙudurin neman beli da Mista Emefiele ya gabatar.

Daga bisani, kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Yuli don yin hukunci kan wannan buƙata.

A ranar 10 ga watan Yuni ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga matsayin Gwamnan Babban Bankin ƙasar, daga bisani kuma hukumar DSS ta sanar da cewa tana tsare da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here