Gwamnan Kano ya nada dansa shugabancin wata hukumar gwamnati

0
158

Gwamnan  Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa ɗansa na riƙo, Ahmad A. Yusuf a matsayin Sakataren Gudanarwa na Hukumar Tarihi da Al’adu ta jihar.

Ahmad A. Yusuf ɗa ne ga shaƙiƙin gwamnan, amma  a hannunsa ya taso har ma ake masa kallon ɗansa na fari.

Idan za a iya tunawa dai, lokacin da gwamnan ke karɓar satifiket na nasarar zaɓensa daga hukumar zaɓe, INEC ranar 29 ga Maris, 2023, gwamnan ya bada tabbacin cewa ba zai sa iyalinsa cikin harkokin mulki ba.

“Babu yadda za a yi in bar iyalina su tsoma baki a harkokin gwamnati ba, saboda ni kaɗai na rantse ba tare da su ba, wato dai su babu su a gwamnati,’” in ji Gwamnan.

Sai dai, a wata sanarwa da Kakakin Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi, Gwamnan ya sanar da naɗa ɗan na sa a muƙamin gwamnati.

Sanarwar ta ce ” Gwamnan jihar Kano Mai girma Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin waɗanann: Arc. Ahmad A. Yusuf, Sakataren Gudanarwa, Hukumar Tarihi da Al’adu ta jihar Kano; Engr. Ado Jibrin Kankarofi, Mataimakin Manajan Darakta, Hukumar Kula da Hanyoyi ta jihar Kano (KARMA), Hauwa Muhammad, Mataimakiya ta Musamman, Harkokin Mata.

“Duk waɗannan naɗe-naɗe sun fara aiki nan take, ” kamar yadda sanarwar ta ƙunsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here