Bournemouth ta nada Iraola madadin Gary O’Neil da ta kora

0
88

Bournemouth ta sanar da nada Andoni Iraola a matakin sabon kociyanta, ya maye gurbin Gary O’Neil da ta kora ranar Litinin.

Iraola, dan kasar Sifaniya, mai shekara 40, ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyu, wanda yarjejeniyarsa ta kare da Rayo Vallecano.

Iraola ya yi kaka uku a Rayo Vallecano a La Liga, wanda ya kai kungiyar mataki na 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da aka kammala.

Bournemouth ta kori Gary O’Neil, kasa da wata bakwai, bayan da aka nada shi a matakin mai horar da kungiyar.

Mai shekara 40 ya fara karbar aikin na rikon kwarya, bayan da aka sallami Scott Parker cikin watan Agusta daga nan ya zama cikakken koci cikin watan Nuwamba.

O’Neil ya ci wasa 10 a karawa 34 da ya ja ragama a Premier League a kakar da ta wuce, inda Bournemouth ta yi ta 15 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.

Bournemouth ta ce nan gaba kadan za ta sanar da wanda zai maye gurbin O’Neil ba tare da bata lokaci ba..

O’Neill ya karbi aikin horar da kungiyar ta Vitality Stadium, bayan korar Parker, sakamakon da Liverpool ta ci Bournemouth 9-0 a Premier League, shine wasan da aka dura kwallaye a raga da yawa a tarihi.

Ya hada maki 13 daga wasa 11 da ya ja ragama, wanda aka bai wa yarjejeniyar kaka daya da rabi da cewar za a iya tsawaita masa ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here