Ba mu ce muna neman Matawalle ba – EFCC

0
139

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ta musanta cewa tana neman Tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle.

Tun da farko wata jarida ce a Nijeriya ta wallafa labarin cewa EFCC na neman Matawalle ruwa a jallo.

Jaridar ta ruwaito cewa wata babbar majiyar tsaro a ranar Lahadi ce ta tabbatar mata da cewa EFCC ta bukaci hukumar DSS ta kama Matawalle kan zargin cin hanci.

Sai dai a sanarwar da hukumar EFCC ta fitar a shafin Twitter, ta nesanta kanta da labarin da jaridar ta buga inda ta ce labarin ba gaskiya ba ne kuma ba ta bukaci wata hukuma da ta kama shi ba.

Hukumar ta ce tana da tsare-tsare da matakan da take bi wurin ayyana cewa tana neman mutum ruwa a jallo ba wai ta “majiyoyin tsaron da ba a san da su ba”.

A kwanakin baya dai an yi musayar yawu tsakanin tsohon gwamnan na Zamfara Bello Matawalle da kuma dakataccen Shugaban EFCC AbdulRashid Bawa.

Hakan ya faru ne bayan zargin almundahana ta naira biliyan 70 da hukumar ta EFCC ke zarginsa a kai, inda shi kuma Matawallen ya zargi Bawa da kokarin karbar rashawa a hannunsa.

Haka kuma a kwanakin baya jami’an hukumar DSS sun kai samame gidan tsohon gwamnan na Zamfara inda suka kwace wasu motoci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here