An kuɓutar da mutum 120 da ke cikin jirgin ruwan da ya kama da wuta

0
120

Jami’an da ke gadin tekun Philippines sun ce sun kuɓutar da mutum 120 da ke cikin jirgin ruwan da ya kama da wuta a tekun da ya raba tsibiran asar

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa jirgin wanda ke ɗauke da fasinjoji 65 da sojoji 55 da kuma ma’aikatan jirgin ya kama da wuta ne a lokacin da yake tafiya a tekun ƙasar kusa da tsibirin Bohol.

Mai magana da yawun jami’an gadin tekun ya ce kawo yanzu ba a san dalilin tashin wutar ba.

Tashin gobara a jiragen ruwa dai ba abu ne da aka saba gani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here