Bayern Munich na tattaunawa kan Walker, PSG na zawarcin Silva

0
101

Bayern Munich na tattaunawa kan dauko ɗan wasan Manchester City da Ingila Kyle Walker, mai shekara 33. (Mail)

Chelsea ta amince da wasu sharuda kan ɗan wasan Villarreal da ke wasa a Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 21. (The Athletic – subscription required)

An bai wa Manchester United damar sayen ɗan wasan Portugal mai shekara 21, Gancalo Ramos daga Benfica kan fam miliyan 80. (Sun)

Chelsea ta yi watsi da tayin Arsenal kan, Kai Havertz sai dai kuma ba a daina tattaunawa kan ɗan wasan na Jamus mai shekara 24 da ke cikin matsuwar barin kungiyar ba.(Telegraph)

Bayern Munich ta bi sahun Arsenal a farautar Havertz. (Sky Sport Germany)

Barcelona ta shiga farautar Ilkay Gundogan na Jamus, wanda kwantiraginsa ya kare a Manchester City. Kungiyar ta yi masa tayin kwantiragin shekara uku. (Athletic – subscription required)

David de Gea, mai shekara 31, na shirin bankwana da Manchester United a wannan kaka. (Mirror)

Ɗan wasan Sweden Dejan Kulusevski, mai shekara 23, ya juya zaman aronsa zuwa na dindindin daga Juventus zuwa Tottenham kan yarjejeniyar fam miliyan 25.6. (90min)

Manchester City na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Croatia, Mateo Kovacic mai shekara 29, kan yarjejeniyar fam miliyan 34 daga Chelsea. (ESPN)

Brighton na son Chelsea ta bata fam miliyan 100 kan ɗan wasanta na tsakiya Moises Caicedo, mai shekara 21. (Athletic – subscription required)

Chelsea kusan ta cimma yarjejeniya da Caicedo. (Fabrizio Romano)

Paris St-Germain na son sayo, Bernardo Silva kuma ta shiga tattaunawa da ɗan wasan na gefe, sai dai Manchester City ba ta shirya rabuwa da shi ba. (Nicolo Schira)

Kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya za ta gabatar da tayi mai gwabi kan ɗan wasan Moroko da ke taka leda a Chelsea Hakim Ziyech, mai shekara 30. (Foot Mercato – in French)

Manchester United da Tottenham na cikin kungiyoyin da suka magantu da wakilinn ɗan wasan Leeds Unite da Jamus Robin Koch, mai shekara 26. (90min)

Ɗan wasan Fulham Tosin Adarabioyo, na cikin ‘yan wasan da Tottenham ke hari a yanzu. (Sky Sports)

West Ham ta gabatar wa Liverpool tayin ba da aron ɗan wasanta Fabio Carvalho, mai shekara 20, yayinda suma Brentford da Burnley ke son a basu ɗan wasan na wucin-gadi.(Football Insider)

Manchester United ta soma tattaunawa da Manchester City a kokarin saye Jack da Tyler Fletcher. (Manchester Evening News)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here