Tottenham na zawarcin Maddison da Barnes, Chelsea da Man Utd na son Onana

0
138

Tottenham ta gabatar da wani tayin haÉ—in-gwiwa na fam miliyan 50 kan ‘yan wasan Leicester City James Maddison mai buga tsakiya da kuma Harvey Barnes da ke buga gaba. (Mail)

Manchester United da Manchester City da Chelsea za su hakura da farautar Declan Rice bayan watsi da tayin Arsenal na fam miliyan 90 da West Ham tayi kan É—an wasan mai shekara 24. (Telegraph – subscription required)

Arsenal ba ci gaba da gwada sa’arta kan Rice, sannan ta janye daga zawarcin É—an wasan Brighton mai shekara 21 Moises Caicedo. (Times – subscription required)

Caicedo ya yanke shawarar tafiya Chelsea, inda ake matakin karshe na daidaitawa. (Sky Sport Germany)

Dan wasan Chelsea da Jamus Kai Havertz, mai shekara 24, ya cimma yarjejeniya da Arsenal, sai dai ba a kai ga daidaitawa ba a kungiyance. (Fabrizio Romano)

Chelsea na fuskantar gasa da Manchester United kan cinikin mai tsaron ragar Inter Milan asalin ƙasar Kamaru Andre Onana, mai shekara 27. (Guardian)

Newcastle United ba ta fid da rai ba a cinikin É—an wasan baya Kieran Tierney, mai shekara 26, duk da barazanar da take fuskanta daga Arsenal. (Football Insider)

Atalanta za ta fuskanci kuÉ—aÉ—e da yawa kan É—an wasanta Rasmus Hojlund, wanda Manchester United da Chelsea ke hari. (Mail)

Liverpool na son É—an wasan Paris St-Germain mai shekara 17 asalin Faransa Warren Zaire-Emery, wanda ke burge kocin Manchester City Pep Guardiola kuma babu mamaki a nemi maye gurbin Bernardo Silva da shi. (RMC Sport, in French)

Arsenal na kan fafutikar neman saye Ilkay Gundogan a wannan kaka, sai dai tsohuwar kungiyar É—an wasan mai shekara 32, Borussia Dortmund ta janye daga farautar É—an kasar Jamus din, da kwantiraginsa ya zo karshe a City. (Bild, in German – subscription required)

Bayern Munich ke kan gaba cikin kungiyoyin da ke neman saye É—an wasan Napoli Kim Min-jae. (Sky Sports)

Kungiyar Saudiyya Al-Tawoon ta gabatar da tayin fam miliyan 50 kan É—an wasan Sifaniya mai shekara 30 Alvaro Morata. (Sport, in Spanish)

Borussia Dortmund ta bi sahun Liverpool da Aston Villa da Burnley a zawarcin É—an wasan Japan Keito Nakamura. (Mail)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here