Na shawarci Tinubu kar ya saki Nnamdi Kanu – Asari Dokubo

0
151

Jagoran Neja Delta, ya shawarci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan kada ya kuskura ya saki jagoran kungiyar ’yan aware ta Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

A cewar Asari Dokubo, bai wa Nnamdi Kanu damar shakar iskar ’yanci zai kasance tamkar yi wa ta’addanci sakayya da tukwici na alheri.

Dokubo ya yi wannan furuci ne a wannan Juma’ar yayin ganawa da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

A cewar Dokubo, dole ne a Nnamdi Kanu ya girbi abin da ya shuka ta fuskar shari’a.

“Sakin Nnamdi Kanu zai zama rashin adalci saboda ya taka rawa wajen rura wutar tashin hankalin da aka gani a lokacin zanga-zangar EndSARS.

“Saboda haka sakin Nnamdi Kanu zai zama tamkar yi wa ta’addanci sakayya da tukwici na alheri bayan tarin jama’ar da aka kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

“Saboda haka dole ne a gurfanar da shi a gaban shari’a domin ya girbi abin da ya aikata.”

A halin yanzu dai Nnamdu Kanu na ci gaba da cin sarka a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, inda ake tuhumarsa da laifin ta’addanci tun bayan sake kama shi da aka yi a shekarar 2021.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce ta bayar da belinsa a shekarar 2017, sai dai daga bisani ya watsa wa kotun kasa a ido ta hanyar kin mutunta sharudan belinsa har ta kai shi ga tserewa daga kasar.

Aminiya ta ruwaito yadda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shafa wa idonsa kwalli kan duk kiraye-kirayen neman sakin jagoran na IPOB.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here