Sama da maniyyata 155 ba za su samu tashi daga jihar Kano ba

0
113

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, ta ce maniyyata 156 ba za su samu tafiya aikin hajjin bana ba sakamakon yawan kujerun aikin hajji da jamiā€™an hukumar da aka kora suka sayar.

Hukumar Alhazai ta kasa ta ware wa Jihar Kano kujeru 6,144 amma hukumar ta sayar da karin kujeru 156.

Babban daraktan hukumar, Alhaji Laminu Rabiu ne ya bayyana hakan a yayin zanta wa da manema labarai a Kano.

Ya ce, za a binciki jamiā€™an da ke da suka gabata tare da gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala aikin hajjin bana.

Rabiā€™u, ya yi kira ga maniyyatan da abin ya shafa da su yi hakuri, ya kuma yi musu alkawarin cewa za a ba su kulawa a aikin hajji mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here