Dokar lamunin dalibai za ta hana da dalibai da yawa damar yin karatu – ASUU

0
120

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta ce kudirin rancen dalibai, wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya wa hannu, na da damar hana da dalibai da dama cigaba da makaranta.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin ne shugaban kasar ya rattaba hannu kan kudirin dokar, inda ya bayyana dokar a matsayin cika daya daga cikin alkawuran da ya dauka a yakin neman zabe.

Amma, Osodeke ya ce dokar na iya yin illa ga miliyoyin daliban da ke son zuwa karatu da suka dogara da manyan makarantun koyo marasa koyarwa don samun ilimi.

Ya ce, “Kasar da sama da miliyan 133 ke fama da talauci kuma kuna son bullo da kudin makaranta? Zai zama mara amfani.

“Ya kamata kowane dan Najeriya ya san abin da zai faru a gaba kuma akwai yuwuwar a samu wani kudirin doka da ke jiran sa hannun wanda zai gabatar da kudin makaranta. 

“Idan kudirin ya nuna cewa rancen zai biya kudin makaranta kuma babu kudin karatu a jami’o’in Najeriya, to menene hanya ta gaba?”

A cewar Osodeke, kudirin ba sabon abu bane, wanda ya bayyana yadda kungiyar ta yi watsi da shi lokacin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo shi.

Sai dai ya yi nuni da cewa har yanzu kungiyar ba ta samu sahihin kwafin dokar da Tinubu ya sanya wa hannu ba, inda ya kara da cewa akwai bukatar a samu tare da yin nazari a kai.

“Mun sha fada a baya, a shekarar 2017 ga Shugaba Buhari lokacin da suka fito da batun kudin makaranta, cewa kowane dalibi zai biya Naira miliyan 1, muka ce ba za ka iya sanya hakan a yarjejeniyarmu ba, kuma ba za ka iya amfani da hakan wajen tattaunawa da mu ba. kuma da yanayin kasar da muke da shi a yau, babu yadda za a yi da zai yi aiki.”

“Abin da zai faru shi ne, yawancin daliban da iyayensu ba za su iya biya ba, za su fice daga makaranta a fusace kuma ka san ma’anar hakan, za su yaki al’umma. Amma bari mu fara samun cikakkun bayanai kafin mu san matakai na gaba,” in ji shi.

A halin da ake ciki, har yanzu ma’aikatar ilimi ta tarayya ba ta yi magana kan sabuwar dokar lamunin dalibai ba.

Amma, ana sa ran ma’aikatar za ta yi jawabi ga taron manema labarai daga baya don fayyace dukkan batutuwan da suka shafi dokar lamuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here