Dan wasan PSG Mbappe ya ce ba zai tafi Real Madrid ba

0
131

Fitaccen dan wasan Paris Saint-Germain (PSG) Kylian Mbappe ranar Talata ya musanta rade-radin da ake yi cewa zai tafi Real Madrid a bazara.

“Karya ce… Wannan babbar karya ce. Tuni na ce zan ci gaba da murza leda a PSG a kakar wasa mai zuwa, inda na fi samun farin ciki,” in ji Mbappe a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Dan wasan gaban na Faransa Mbappe, mai shekara 24, ya koma PSG ne daga Monaco a 2018 a yarjejeniyar dindindin bayan ya yi zaman aro a kungiyar na kakar wasa daya.

A 2022, Mbappe ya tsawita yarjejeniyarsa a PSG zuwa 2025, a yayin da ake rade-radin cewa zai tafi Real Madrid a kakar wasa ta 2021-22.

Tun da farko jaridar Le Perisien ta kasar Faransa ta yi ikirarin cewa Mbappe zai tafi Real Madrid a bazara bayan Karim Benzema ya bar PSG.

A makon jiya, Benzema ya yi bankwana da Real Madrid inda ya tafi kungiyar kwallon kafar Al-Ittihad ta kasar Saudiyya.

Mbappe yana cikin manyan ‘yan wasan Faransa da PSG domin kuwa ya taimaka wa kasar ta dauki Kofin Duniya na 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here