Abba Gida-Gida: Abin da ya sa na rusa shataletalen gidan gwamnatin Kano

0
205

Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya ce sun rusa shataletalen kusa da gidan gwamnatin jihar ne saboda barazanar tsaro da ke tattare da kasancewarsa a wurin.

A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamnatin jihar ya fitar ranar Laraba, ya ce sun rusa shataletalen ne “saboda kare muradun al’umma.”

An rusa shataletalen ne, wanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta gina, jiya da daddare lamarin da ya jawo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar.

Mutane da dama na ganin gwamnati ta dauki matakin ne da zummar muzanta wa tsohon Gwamna Ganduje.

Amma sanarwa da Sanusi Dawakin Tofa ya fitar ta ce “kafin rusa ginin, gwamnati ta tattauna da kwararrun injiniyoyi wadanda suka tabbatar da cewa an yi amaja wajen gina shataletalen da kuma yiwuwar rushewarsa a shekarar 2023 ko 2024.

Hakan zai faru ne saboda an gina ta ne da katifun da aka taba amfani da su da kuma kasa mai yawa maimakon kankare.”

Gabanin fitar da sanarwar gwamnatin, mutane sun rika tsokaci game da rusa fitaccen shataletalen.

Hotunan da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta sun nuna manyan motocin katafila suna rusa shatale-talen, wanda rahotanni suka ce an yi aikin a tsakar daren ranar Talata.

Sabon gwamnan jihar ta Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ake kira Abba Gida-Gida, wanda ya sha rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, ya sha nanata cewa zai rusa duk ginin da aka yi ba tare da bin doka ba.

Tuni gwamnatinsa ta rusa gine-gine a Kofar Nasawara da Hajj Camp da Masallacin Idi da wasu wuraren, lamarin da ya jawo masa yabo da suka daga mutane daban-daban.

Rashin tunani

Sai dai matakin rusa shataletalen, wanda aka wayi garin Laraba da shi, ya ja hankalin ‘yan kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

Galibin wadanda suka yi tsokaci kan batun, ciki har da masu goyon bayan gwamnatin ta Kano sun bayyana matukar bacin ransu game da wannan mataki.

Fitaccen dan jaridar nan Jaafar Jaafar, ya bayyana cewa yana goyon bayan matakin da gwamnatin Kano take dauka na gyara barnar da gwamnatin baya ta yi, amma ban da wannan.

 

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce “dole ne mu yi tir da wannan matakin rashin tunani na rusa wannan wuri na musamman, wanda wata matashiyar mai zana gine-gine ta yi don bikin cikar Kano shekara 50.

Ina goyon bayan rusau din da ake yi a yanzu na gine-ginen da mutane suka yi a cikin makarantu da asibitoci da masallatai, amma ban da na wurare na musamman, kawai don Ganduje ne ya yi su,” in ji Jaafar.

Shi ma wani magoyin bayan kungiyar Kwankwasiyya, T.M Bichi, ya ce a matsayinsa na kwararren mai tsara birane, ba ya goyon bayan rusa ginin saboda “barnatar da kayan gwamnati ne”.

 

Sai dai a nasa bangaren, Asad Mukty, ya kare matakin gwamnatin Kano yana mai cewa “akwai randabawul kafin wannan, Ganduje ya kashe kusan naira miliyan 100 a kan wannan, ya gina ta bisa tsari irin nasa.

Yau, Abba ya zo ya ga ba ta dace ba, kuma barna da cuta ce.”

Shi ma Murad Faisal ya ce bai ga laifin gwamnati na rusa wurin ba yana mai cewa “yawancinku kuna kallon batun ne ta fuskar kyawun ginin, amma kun manta da kura-kuran da aka yi wajen ginin.

Ana samun babban cunkoso inda masu ababen hawa kan shafe awanni kafin su wuce ta wurin. Hakan babbar barazana ce ga gidan gwamnatin jihar,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here