Tinubu bai bude iyakokin Najeriya ba – Kwastam

0
140

Hukumar Hana Fasa Kauri ta Kasa (Kwastam) ta ce har yanzu shugaban kasa Bola Tinubu bai sake bude dukkan iyakokin kasar nan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta rufe ba.

Idan za a tuna a shekarar 2019 ne, Buhari ya rufe dukkan iyakokin kasar nsn domin hana shigo da wasu kaya ba bisa ka’ida ba, wadanda suka hada da shinkafa, bindigogi da sauransu.

Bayan shekaru biyu, gwamnatin Buhari ta sake bude wasu kadan daga cikin iyakokin, wasu kuma sun kasance a rufe duk da kokawar da ‘yan Nijeriya suka yi.

A kwanakin baya ne wasu mutane suka fara yada wani tsohon faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka ga Konturola na hukumar NCS reshen Ogun, Bamidele Makinde ya bude shingen da ke kan iyakar Idiroko da Jamhuriyar Benin.

An yada bidiyon tare da cewa Tinubu ya sake bude iyakokin kasar nan.

Da yake mayar da martani, Konturola na NCS ya ce gwamnatin Tinubu ba ta ba da umarnin sake bude dukkan iyakokin kasar nan ba.

A cewarsa, gwamnatin Buhari a shekarar 2022 ta sake bude iyakar Idiroko da wasu ‘yan tsiraru, inda ya ce sauran na ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu karin umarni daga gwamnatin tarayya.

Bamidele ya bayyana cewa, sauran iyakokin da aka amince da su a jihar Ogun kamar Ijofin, Imeko, Ijoun da kuma Ohunbe na nan a kulle.

“Idiroko ne kawai aka bude yanzu; sauran kuma har yanzu a kulle suke,” in ji shi.

Makinde, yayin da yake zanta wa da manema labarai a Abeokuta, ya ci gaba da cewa jami’an Kwastam ma’aikatan gwamnati ne, wadanda aikinsu shi ne aiwatar da manufofin gwamnati.

“Yanzu, muna da sabuwar gwamnati. Sabuwar gwamnati za ta zo da manufofinta. Bai kamata a sami kuskure ba. Mu ma’aikatan gwamnati ne kawai, muna aiwatar da manufofi. Duk abin da Abuja ta ce muna yi,” a cewarsa.

Ya jaddada cewa, “Iyakar Idiroko na bude ko fa yaushe, amma a sauran idan muka kama mutum za mu kwace kayansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here