Manyan ƙalubalen da Majalisa ta goma za ta fuskanta a Najeriya

0
108

Ranar Talatar nan ne ake ƙaddamar da majalisar tarayya ta goma a Najeriya, wadda za ta ci gaba da ayyukan kafa dokoki da bibiyar harkokin ɓangaren zartarwa a ƙasar.

Majalisar na ɗaya daga cikin ɓangarorin mulki uku da tsarin mulkin ƙasar ya samar, don tabbatar da rabon iko daidai da kuma taka wa juna burki, a inda wani ɓangare ke neman wuce gona da iri.

Muhimmin matsayin da Majalisar Tarayyar ke takawa a Najeriya ne ya sanya ta zama ginshiƙi wajen gudanar da harkokin duk wata gwamnati da kuma samun nasarar cika alƙawurra da manufofin da ta zo da su, ko kuma akasin haka.

Wasu ‘yan Najeriya sun soki majalisar da ta shuɗe a kan abin da suka kira tsananin ba da haɗin kai ga ɓangaren zartarwa, inda suka yi zargin cewa hakan ya sanya ta kawar da kai ga wasu muradan al’umma da abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

Haka zalika, wasu masu ruwa da tsaki ciki har da su kansu ‘yan majalisar sun nunar cewa majalisar ta yi fama da ɗumbin matsaloli ciki har da rashin bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa yadda ya kamata, da ƙarancin kuɗin gudanar da ayyuka da sauransu.

To ita fa majalisa ta goma da za a ƙaddamar, ko waɗanne ƙalubale za ta iya fuskanta a tsawon aikinta na shekara huɗu?

Wakilci

Wata muhimmiyar manufa ta mulkin dimokraɗiyya ita ce tabbatar da ganin an bai wa kowa dama domin ya shiga cikin harkokin gwamnati a dama da shi. Hakan zai tabbata ne a cewar ‘yan fafutuka ta hanyoyi da dama ciki har da ba da wakilci nagari.

Dr El-Harun Muhammad ya ce wajibi ne ‘yan majalisa ta goma su fahimci cewa su wakilai ne, su je zauren majalisar ne saboda jama’a sun zaɓe su don yin wakilci.

“Sun zo ne su gabatar wa gwamnati koke-koke da matsalolin mutane.” A cewarsa wannan shi ne muhimmin aiki da ya kamata su sanya a gaba.

Shi ma ɗan fafutuka, Auwal Musa Rafsanjani ya ce shigar da al’umma cikin ayyukan majalisa ta yadda za a riƙa jin ra’ayoyinsu, abu ne mai matuƙar tasiri ga dokokin da za ta samar a tsarin dimokraɗiyya.

“Ya zamto ‘yan ƙasa an ba su dama su tofa albarkacin bakinsu cikin harkar tsara doka ko wata manufar gwamnati da za ta amfani ƙasa,” in ji shugaban ƙungiyar CISLAC.

A cewarsa, jazaman ne majalisa ta goma ta tabbatar tana gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a don jin tsokaci daga masu ruwa da tsaki kafin yin doka.

El-Harun ya ce majalisa ta goma za ta iya tabbatar da manufar ba da wakilci nagari ta hanyar tuntuɓar mutanen da take wakilta a kai a kai, da kai musu bahasi don sanar da su game da ayyukan da take yi.

Shugabanci

Ga dukkan alamu, babban ƙalubalen da Majalisar Tarayya ta goma za ta yi fama da shi, da zarar an ƙaddamar da ita a Talatar nan, shi ne batun mutanen da za su jagorance ta.

Wannan muhimmin al’amari ne a Najeriya, kuma tuni yake ci gaba da ta tayar da ƙura a fagen siyasar ƙasar.

Cikin manyan masu neman takarar shugabancin majalisar dattijai ta goma, akwai Sanata Godswill Akpabio wanda jam’iyya mai mulki ta APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suke mara wa baya.

Yana takarar ne tare da Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai.

Sai dai Sanata Abdul’aziz Yari daga jihar Zamfara na cikin waɗanda su ma suke neman shugabancin. ‘Yan majalisa 109 ne za su kaɗa ƙuri’a don zaɓar mutumin da zai jagorancin majalisar.

A mafi yawan lokuta, irin shugabannin da aka zaɓa ne za su haska salon yadda dangantaka za ta kasance tsakanin ɓangaren zartarwa da masu yin dokar. Irin wannan zaɓe, a 2015, ya bar baya da ƙura, inda aka yi zaman doya da man ja tsakanin gwamnatin Shugaba Buhari da shugabancin majalisa ta takwas a kusan tsawon shekara huɗu.

  • 12 Mayu 2023

Ga alama dai a wannan karo, lamarin ina iya ƙara zama mai sarƙaƙiya saboda shugaban ƙasar da jam’iyya mai mulki tuni suka bayyana goyon bayansu ga Akpabio, Kirista daga Kudancin Najeriya.

A cewarsu, matakin zai tabbatar da daidaito da shigar da kowanne ɓangare a dama da shi cikin gwamnatin da shugabanta da mataimakinsa duka ke wakiltar addini ɗaya, wato Musulunci.

Matakin dai ya saɓawa abin da aka saba gani a siyasar Najeriya.

A Majalisar Wakilai ma, har yanzu akwai ‘yan majalisar da ke ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki wadda ta nuna goyon bayanta ga Hon Abbas Tajuddeen a matsayin wanda take so ya kasance shugaba.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai Hon Ahmed Idris Wase na cikin masu neman takarar.

Dokokin kawo gyara da bunƙasa rayuwa

Wani babban aikin ‘yan majalisar dokoki shi ne samar da dokokin da za su taimaka wajen inganta rayuwa da tabbatar da ci gaban ƙasa da kuma kawo sauƙi ga al’umma.

Mallam Awwal Musa Rafsanjani ya ce akwai dokoki da yawa da ake sa ran gani ‘yan majalisar ta goma sun kawo a cikin shekara huɗu masu zuwa.

Halin ƙaƙa-ni-ka-yi da matsin rayuwar da ‘yan Najeriya suke ciki saboda gurɓataccen shugabanci da kuma tsarin tattalin arziƙi a cewar Dr El-Harun Muhammad na cibiyar tsara manufofi da raya ƙasa da kuma ƙirƙire-ƙirƙire, wasu ɓangarori ne da ‘yan ƙasar za su zuba ido cikin gaggawa su ga an ɓullo da matakan rage musu raɗaɗi.

Ya ce bisa dukkan alamu, ita ma gwamnati mai ci za ta ɗora ne a kan manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin da ta gabata. A cewarsa, wajibi ne majalisar ta riƙa duba a kan waɗanne ne muhimman buƙatun ‘yan ƙasa da kuma me ya kamata a yi musu don inganta musu rayuwa.

Yayin da Auwal Rafsanjani ya ce dokokin da ake buƙata a ƙasar sun haɗar da yi wa tsarin mulkin Najeriya garambawul da ƙarfafa dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa, sai gyara dokokin karɓar haraji da dokokin inganta aikin ɓangaren shari’a da bunƙasa harkokin kula da lafiya.

Ya kuma ce dokokin ɓangaren tsaro ma, na cikin abubuwan da ke buƙatar a ƙarfafa su don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar.

Tasirin ƙabilanci da addini

Dr El-Harun Muhammad ya ce batun ƙabilanci da addini na cikin manyan ƙalubalen da majalisa ta goma za ta fuskanta.

A cewar daraktan waɗannan al’amura sun yi katutu a fagen siyasar Najeriya, ta yadda suke tasiri a naɗe-naɗen shugabanci da rabon muƙamai.

Ya ce matsalar ta yi ƙamari har a ɓangaren zartarwa da kuma a cikin majalisar dokokin ƙasar, inda ake ta kai ruwa rana game mai bin wanne addini ne zai zama shugaban majalisar dattijai da kuma ta wakilai.

Dr. El-Harun ya ce lamarin babban ƙalubale ne wanda ya kamata, sabuwar majalisar ta mayar da hankali a kai don magancewa.

Bincike

Wasu ‘yan fafutuka a ƙasar kamar shugaban ƙungiyar bunƙasa wayar da kai game da ayyukan majalisa (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani na ganin babban ƙalubalen da ke gaban majalisa ta goma shi ne bincike.

Ya ce gwamnatoci a Najeriya sun fi son ganin ‘yan majalisa sun karɓa tare da amincewa da duk wasu buƙatu da ƙudurorin doka da suka gabatar musu ba tare da sun yi tambaya ko gudanar da bincike ba.

“Gwamnati mai zartarwa ta fi son aiwatar da buƙatunta, ba tare da majalisa ta tsaya ta yi tunani da nazari a kan ko ya kamata a amince da su ko bai kamata ba,” in ji shi.

A cewarsa rashin bincike ko yin nazari kan wasu manufofi ko buƙatun ɓangaren zartarwa, kan sa a wasu lokutan majalisar ta amince da abin da zai kasance mai nakasu ga al’ummar ƙasar maimakon wanda zai amfane su.

A baya-bayan nan, an jiyo wani jigon ɗan majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume na kokawa a kan yawan haɗin kan da suka bai gwamnatin da ta wuce, wadda aka zarga da yawan ciyo basukan da wasu ke cewa sun zame wa najeriya alaƙaƙai.

Sanatan ya ce ba su gudanar da binciken da ya dace sosai ba, sannan ba su yi nazarin amfanin karɓo basukan ba.

Haka zalika ba su tantance amfanin basukan da aka karɓa a baya ba, da yadda za a biya kuɗin da aka ciyo bashin ba, da kuma abubuwan da za su iya biyo baya.

Gujewa zama Ƴan amshin shata

Wani abu da aka fi sukar majalisun tarayyar Najeriya game da shi, shi ne zama ‘yan amshin shata.

Majalisu ne da ba a cika jin suna taka burki ga ɓangaren zartarwa ba, kuma sukan gaza wajen nuna bijirewa ga duk wani aiki ko buƙata ko wata manufar gwamnati da mai yiwuwa za ta iya cin karo da muradun ‘yan ƙasar.

Masu ilmin kimiyya dai sun yi ittifaƙin cewa duk da yake akwai buƙatar a samu haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa don aiwatar da muradu da ƙudurorin bunƙasa rayuwar ‘yan ƙasa, amma akwai buƙatar majalisar ta zama mai kare muradan jama’ar da take wakilta maimakon buƙatun shugabanni kawai.

Dr El-Harun ya ce bai kamata a ce majalisa ta zama kamar ƴar amshin shata ba, a cewarsa, gaɓa ce ta gwamnati wadda wani bai fi wani ɓangare ba.

“Bai kamata a ce majalisa ta zama ‘yar amshin shata ba,” in ji masanin.

Gaɓoɓin gwamnati guda uku ɓangaren zartarwa da na shari’a da kuma na yin doka, in jishi ɗaya bai fi ɗaya.

Waɗannan su ne gaɓoɓi da za a tafiyar da gwamnati a kan gaskiya, a kan adalci da kuma a kan tafarkin wakiltar jama’a, Dr El-Harun ya ce.

Yayin da Rafsanjani ke cewa matuƙar majalisa ta goma ta mayar da kanta ‘yar amshin shata, to ba shakka tana iya fuskantar matsala da jama’ar da take wakilta.

Bibiyar ayyukan ma’aikatu da hukumomi

Mallam Auwal Rafsanjani ya ce wani muhimmin ƙalubale da ‘yan Najeriya suke sa ran ganin canji daga majalisa ta goma shi ne inganta bibiya da bin diddigin ayyukan ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Majalisun da suka gabata a Najeriya sukan fuskanci suka bisa zargin gazawa wajen bibiyar ayyukan da ɓangaren zartarwa da kuma yadda suke kashe kuɗaɗe da majalisar ta keɓewa hukumomi da ma’aikatu.

Auwal Musa Rafsanjani ya ce majalisar bisa doka tana da ƙarfin da za ta taka burki ga duk wata hukuma ko ma’aikata da ta karkace wajen gudanar da aikinta. A cewarsa, majalisar kuma za ta iya tabbatar da haka ne idan ta tsare ƙimarta ta hanyar gujewa zuwa roƙo a hukumomi da ma’aikatun gwamnati.

Ɗan rajin yaƙi da cin hancin ya ce matuƙar ‘yan majalisar na da burin yin aiki tsakaninsu da Allah, to sai sun gujewa zuwa roƙo wajen ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.

A cewarsa irin wannan roƙon yana zubar musu da mutunci har ya sa ma a raina su.

Yaƙi cin hanci da rashawa

Auwal Musa Rafsanjani ya ce wani ɓangare da ‘yan Najeriya ke zuba ido su ga sauyi daga majalisa ta goma shi ne kan batun yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ce majalisar da ta wuce ta kafa tare da ƙarfafa wasu dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa, sai dai duk da haka samu nasara sosai wajen aiki da dokokin ba.

A cewarsa jazaman ne sabuwar majalisar ta dage wajen tabbatar da ganin ana bin dokokin da aka kafa matuƙar kuma ba haka ba, to da wuya a iya samun wani ƙwaƙƙwaran canji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here