Arsenal ta kusan daukar Declan Rice – Rahotanni

0
144

Arsenal na daf da amincewa da yarjejeniyar daukar Declan Rice daga West Ham kan fam miliyan 100 in ji jaridar the Guardian.

Rice, mai shekara 24 kuma dan kwallon tawagar Ingila na iya koma wa Arsenal da tsada, idan aka hada da tsarabe-tsarabe.

Arsenal din a shirye take ta dauki matashin a matakin mafi tsada da za ta saya a tarihin kungiyar.

Rice dan kwallon tawagar Ingila ya fara tamaula daga karamar kungiyar West Ham daga baya ya koma babbar kungiyar ranar 1 ga watan Yulin 2016.

West Ham United ta tabbatar cewar Rice zai bar kungiyar a karshen kakar nan.

Dan wasan ya lashe Europa Conference League a bana tare da West Ham, bayan da su ka ci Fiorentina 2-1.

Arsenal, wadda ta kare a mataki na biyu a teburin Premier League za ta buga Champions League a kaka mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here