Najeriya na sahun kasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa – Bankin Duniya

0
136

Bankin Duniya ya sanya Najeriya a sahun kasashen da ke fuskantar barazanar yunwa sakamakon tsananin karancin abincin da kasar za ta gani a bana wanda ke da nasaba da sauyin yanayi da zai haddasa fuskantar gajeruwar damuna.

Cikin wani rahoto da Bankin Duniyar ya fitar da ke nuna jerin kasashen da za su fada cikin matsalar ta karancin abinci, ya nuna yadda Najeriya ta shiga sahun kasashen Afghanistan da Somalia da Sudan ta kudu da kuma Yemen da ke matsayin ‘yan gaba-gaba da suka shafe shekaru suna fama da wannan matsala ta karancin abinci sakamakon ko dai gajeruwar damuna ko kuma yake-yake da suka hana iya noma a kasashen.

A cewar rahoton na bankin duniya, dole ne Najeriya ta dauki matakan dakile wannan matsala da ke tunkaro ta yawan jama’arta da wannan matsala za ta shafa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Najeriya ke shiga wannan matsala ba, sai dai a wannan karon bankin ya koka da yadda matsalar za ta tsananta tsakanin watan da muke ciki na Yuni zuwa Nuwamban shekarar nan.

Rahoton na bankin Duniya, ya ce sauran kasashen da wannan matsala za ta shafa sun kunshi Haiti da Sudan da Burkina Faso baya Mali wadanda za su ga matsananciyar matsalar ta karancin abinci.

Bankin ya ce jihohin Borno da Yobe su ne kan gaba a Najeriya da za su gamu da wannan matsala ta karancin abinci, yayinda jihohin Katsina da Sokoto da kuma Zamfara baya ga Kaduna za su bi bayansu.

Hukumar kididdiga ta Najeriya cikin wasu alkaluma da ta fitar a watan Aprilun da ya gabata, ta ce matsalar karancin abinci za ta kai matsayin maki 24 cikin dari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here