Boko Haram ta yi garkuwa da mutane 30 a gabar tafkin Chadi

0
139

Mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da wasu mutum 30 a kusa da Tafkin Chadi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Bayanai na cewa mayakan na neman kudin fansa domin a sako wadanda lamarin ya shafa, kamar yadda masunta da shugaban kungiyar masu yakar ’yan tada kayar baya suka shaida.

Majiyar ta ce mayakan da ke cikin kwale-kwale 8 sun kai farmaki kauyukan Tudun Kwastan da Kwatar Turare da kuma Kwatar Kuwait da ke gabar tafkin a ranar Juma’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mayakan sun kama mutum 30 da suka hada da maza da mata da suka fito kamun kifi da kuma kiwon dabbobinsu a gabar tafkin.

“’Yan Boko Haram sun je wasu kauyukan Fulani inda suka tafi da maza da mata 30,” Labo Sani, wani mai kamun kifi daga Doron Baga, ya tabbatar da hakan kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya bayyana.

“Sun bar sakon da ke neman iyalan wadanda lamarin ya shafa su tara naira miliyan 20 (dala 43,000) kafin a sako su,” in ji Labo.

Mayakan sun bukaci a kai kudin fansa a tsibirin Musaram, inda za a sako mutanen ga iyalansu, in ji Sallau Arzika, wani masunci.

Tun bayan ballewar kungiyar ISWAP daga kungiyar Boko Haram a shekarar 2016, ta kwace iko da mafi yawan yankuna daga hannun ’yan Boko Haram, ciki har da kewayen Tafkin Chadi, inda a yanzu take da karfi.

Kungiyar ta bai wa masunta da makiyaya damar kamun kifi da kiwo a yankinta da sharadin biyan haraji, inda ta samar mata da makudan kudade, inji masuntan biyu.

Kungiyar Boko Haram da ba ta da irin wadannan hanyoyin samun kudin shiga, ta na neman kudi, inda ta yanke shawarar sace makiyayan domin su karbo musu kudi, in ji mayakan da ke yaki da jihadi a yankin.

“An yi garkuwa da mutanen ne saboda kudi kawai, kuma muddin makiyayan suka tara kudin da Boko Haram suka nema, za a sako wadanda aka yi garkuwa da su,” in ji shugaban mayakan.

Amma ya yi gargadin cewa biyan kudin fansar ba zai kawo karshen satar mutane ba.

“Makiyayan Fulani da ke yankin Doron Baga sun fara ficewa ne saboda fargabar sake kawo musu hari ko a yi garkuwa da su,” in ji shugaban kungiyar.

Rikicin jihadi, wanda ya faro a shekarar 2009, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba kimanin miliyan biyu da muhallansu a yankin Arewa maso Gabas, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Sabon Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda aka rantsar a karshen watan Mayu a matsayin shugaban kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka kuma mafi karfin tattalin arziki a nahiyar, na fuskantar kalubalen tsaro da dama.

Kamar magabatansa, ya yi alkawarin bayar da fifikon gaske a fagen yaki da matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here