Zan tafi Inter Miami: Lionel Messi

0
148

Fitaccen dan wasan kwallon kafa Lionel Messi ya tabbatar da cewa zai tafi kungiyar Inter Miami da ke Amurka bayan barinsa PSG a wani mataki na ba-zata.

Messi ya tabbatar da hakan ne a hira d ya yi da jaridun Sifaniya na Diario Sport and Mundo Deportivo, kyaftin na Argentina “Na yanke shawarar tafiya Miami, ba mu kammala yarjejeniya dari bisa dari ba, amma mun amince mu ci gaba da harkar [kwallon kafa] a can.”

Ita ma kungiyar ta Inter Miami ta tabbatar da cewa dan wasan da ya lashe ballon d’or sau bakwai zai tafi can don murza leda.

Daya daga cikin masu kungiyar Jorge Mas ya wallafa wani hoto a shafinsa na Twitter da ke dauke da alamar inuwar rigar Inter Miami da aka rubuta ‘Messi 10’.

“[Na yanke shawarar] barin Turai … bayan na dauki Kofin Duniya kuma ba zan samu damar komawa Barca ba, don haka lokaci ya yi da zan tafi MLS domin na murza leda a hanya ta daban sannan na ji dadin rayuwata a kullum,” in ji Messi.

Messi, mai shekara 35, ya samu tayi na makudan daloli daga kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya da kuma yiwuwar komawa Barcelona amma ya yi watsi da su.

Barcelona ta yi wa dan wasan fatan alheri sai dai ta ce ‘yan kallo ba sa sha’awar wasan da ake yi a kingiyoyi irin su Inter Miami sosai.

Dan wasan na Argentina ya bar PSG a wani yanayi na rashin jin dadi bayan ya murza leda ta tsawo shekara biyu a kungiyar da ke Faransa, wadda ya taimaka wa wurin lashe Ligue 1.

Messi ya zura kwallo 32 a wasanni 75 da ya fafata a kungiyar – kuma ya kammala kakar wasa ta bana da cin kwallo16 sannan ya taimaka aka ci kwallo 16 a Ligue 1.

A 2021 dan wasan ya bar Barca bayan ya kwashe shekara 21 yana murza leda inda ya samu nasarori daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here