Tinubu ya rantsar da George Akume a matsayin sakataren gwamnati

0
121

Shugaba Bola Tinubu, ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya, SGF, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suka halarta a takaitaccen taron a yau (Laraba) sun hada da gwamnan jihar Benue, Rev. Fr. Hyacinth Alia, wasu masu rike da mukamai da tsofaffin gwamnoni, ciki har da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Almakura da tsohon SGF, Boss Mustapha.

Sauran sun hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan; Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr FolasadeYemi-Esan da matar sabon SGF, Misis Regina Akume.

In za ku tuna cewa tun farko Tinubu ya bayyana nadin tsohon gwamnan jihar Benue a matsayin sabon SGF.

Shugaban ya kuma nada kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikata, da kuma Sanata Ibrahim Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.

An bayyana nadin ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye ya fitar a Abuja.

A cewar sanarwar, shugaban ya bayyana nadin ne a yayin ganawar da ya yi da Progressive Governors Forum (PGF), a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.

Akume ya kasance tsohon ministan ayyuka na musamman a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here