An samar da maganin rage mutuwar masu cutar kansa

0
165

An samar da wata kwayar maganin da ke rage barazanar rasa ran masu dauke da cutar kansar huhu, idan ana amfani da maganin a koda yaushe bayan gudanar da tiyatar cire kwayar cutar, kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi ya nuna. 

A lokacin bayyana sakamakon gwajin maganin da aka yi a babban taron shekara-shekara na kwararru a bangaren cutar kansa, wanda wata kungiyar kwararru a Amurka ta shirya a Chicago, an bayyana cewar cutar kansar huhu na sanadin mutuwar mutane kimanin miliyan daya da dubu dari 8 a duk shekara a fadin duniya.

An yi gwajin ne ga mutane 680 a kasashe sama da 20, kuma sakamkon ya nuna cewar kashi 51 na wadanda suke shan magani kullum ba sa fuskantar barazanar rasa ransu, idan aka kwatanta da wadanda suke sha lokaci-bayan lokaci.

Haka nan sakamakon ya nuna cewar kaso 88 na wadanda suke amfani da maganin a kullum sun ci gaba da rayuwa bayan shekaru biyar, idan aka kwatanta da kashi 78 ne kadai na wadanda ke amfani da maganin jifa-jifa suka tsira.

Kamfanin hada magunguna na AstraZeneca ne ya samar da kwayar maganin da ya sanyawa suna Tagrisso. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here