Shanun Buhari sun ragu saboda kyauta’

0
121

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya miƙa takardar da ya cike da ke ƙunshe da bayanan kadarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa’ar ma’aikata CCB bisa tanadin shafi na shida na Kundin tsarin mulkin ƙasa.

Mai magana da yawun tsohon Shugaban, Garba Shehu cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce a yau ne hukumar ta CCB ta tabbatar da karɓar fom din tsohon shugaban ƙasar.

A cewarsa, takardar bayanan ta nuna cewa kadarorinsa da za a iya sauyawa wuri ba su ƙaru ba – a gida da kuma wajen Najeriya.

Sannan bai buɗe wani sabon asusun banki ba, baya ga wanda yake da shi a bankin Union a Kaduna.

Garba Shehu ya ƙara da cewa, tsohon Shugaban bai karɓi bashi ba kuma adadin shanunsa sun ragu saboda ya bayar da wasu kyauta cikin shekara huɗu da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here