Cire tallafin mai: Cigaban Najeriya na buƙatar tsauraran matakai – Wike

0
109

Tsohon gwamnan jihar River da ke kudu maso kudancin Najeriya Nyesom Wike ya kare matakin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur, yana mai cewa mulkin ƙasa irin Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba.

Mista Wike ya bayyana haka ne ranar Juma’a a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja.

Rahotonni sun ce Mista Wike tare da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori sun gana da shugaban ƙasar a wata ziyara da suka kai fadar shugaban ƙasar ranar Juma’a.

Mista Wike ya ce sun je fadar shugaban ne domin mara masa baya kan matakan da yake ɗauka a gwamnatinsa.

”Wannan ya nuna cewa sabon shugaban ƙasa a shirye yake wajen gudanar da mulkinsa, kuma babu aibi dangane da matakin cire tallafin man fetur, domin dole sai an ɗauki tsauraran matakai idan ana so ƙasar ta ci gaba”, in ji Wike.

A watan da ya gabata shugaba Tinubu ya yaba wa tsohon gwamnan na jihar Rivers a wata ziyarar aiki da ya kai jihar, karon farko tun bayan zaɓensa a matsayin shugaban ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here