Abin da ya sa cin zaben Erdogan ya zama nasara ga Afirka

0
134

Babu wani shugaba da ke wajen nahiyar Afirka da ya damu da al’amuran nahiyar kamar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, kuma hakan ne ya sa ‘yan Afirka suka yi farin ciki bayan da ya samu nasarar cin zabe a zagaye na biyu.

Daga Nijeriya zuwa Somaliya; Aljeriya zuwa Afirka ta Kudu, a fili yake Erdogan ya yi ayyukan ci-gaba da kawo ci-gaban tattalin arziki da daidaituwar shugabancin siyasa.

Adamu Usman daga jihar Gombe a arewa maso gabashin Nijeriya ya yi farin ciki a kafar sada zumunta bayan Erdogan ya samu nasara a zabe, inda ya bayyana shugaban Turkiyyar da “gwarzonmu ‘yan Afirka”.

Mohamed Abdi daga Somaliya ya taya Erdogan murna a kan nasarar da ya samu, inda ya ce shugaban Turkiyya ya “bunkasa ta da kawo mata nasara”.

Abdi ya ce a matsayinsa na dan Somaliya ya ce shi kansa ya san irin “‘yan uwantaka da kaunar” da gwamnatin Erdogan take nunawa.

An rika ganin miliyoyin sakonnin taya murna a intanet – daga shugabannin kasashe da dama da mazauna kasashe – inda suka rika yaba wa Erdogan a kan nasarar da ya samu ta cin zabe, kowanensu ya bayyana irin tasirin da shugabancinsa ya yi.

Shugaban Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya wallafa a shafin Twitter cewa nasarar da Erdogan ya samu a zabe za ta kara “karfafa dangantakarmu don amfanin al’ummarmu.”

Sabon kwarin gwiwa

Amma me ya sa nasarar Erdogan take da muhimmanci ga kasashen Afirka? Gitile Naituli wani farfesa ne a bangaren mulki da shugabanci na Jami’ar Multimedia da ke kasar Kenya, ya ce ci gaba da shugabacin Erdogan “alheri ne sosai ga Afirka”.

“Nasararsa za ta ba Turkiyya damar kara fadada ayyukanta a Afirka. Tsawon shekaru nahiyar ta amfana sosai daga Turkiyya kuma hakan ya samu ta hannu Erdogan,” in ji shi.

Malamin jami’ar ya ce da duk alama sabon shugaban “ya kwashe lokaci mai tsawo yana karantar halin da Afirka da mutanenta ke ciki da kuma bukatunsu.”

“A Kenya alal misali, yawancin kanana da matsakaitan masaku suna sayo kayayyakinsu ne daga Turkiyya. Jirgin saman kasar na Turkish Airlines ya zuwa kasashe da dama a nahiyar, kusan fiye da kowane kamfanin jirgin sama na ketare kuma ana ganin karin fasinjoji masu shiga da kuma fita daga Turkiyya.

Nasarar da Erdogan ya samu tana nufin irin wannan cinikayyar da kasuwanci zai ci gaba ne,” in ji Naituli.

Macharia Munene, farfesa ne a fannin nazarin hulda da kasashe a Jami’ar Amurka da ke Afirka, ya ce nasarar da Erdogan “za ta ba shi gwarin gwiwa don ci gaba da ayyuka daban-daban da ya kaddamar a Afirka.”

“Nasarar ba kawai za ta ba shi damar bunkasa Turkiyya ba, amma hakan zai ba shi damar fadada ayyukansa a bangaren kasuwanci da diflomasiyya,” in ji Munene.

Turkiyya ta yi aiki a Afirka a bangarori da dama ciki har da tattalin arziki da diflomasiyya da tsaro da ayyukan jin kai da ilimi da kiwon lafiya.

Lokacin da Erdogan ya rike mukamin firaiminista tsakanin shekarar 2003 zuwa 2014, ya dasa harsashin kulla yarjejeniya da kasashen Afirka.

Don yaukaka dangantakar, ya kai ziyara akai-akai kasashen Afirka kamar su Chafi da Somaliya da Sudan da Tunisiya da Senegal da Ethiopia da Angola da Nijeriya da Togo a matsayinsa na shugaban kasa, adadin kasashe mafi yawa da wani shugaba ya taba ziyarta.

Arzikin da ke kwance a Afirka

Naituli ya ce Shugaba Erdogan ya na da “basira” dangane da yadda ya “fahimci arzikin kasuwancin da ke kwance a Afirka.”

“Nahiyar tana da mutane fiye da biliyan 1.4 kasuwace da ke habbaka wacce ba a gama bunkasa ta ba. Erdogan ya fahimci haka shi ya sa ya mayar da hankali a kan haka,” in ji shi.

Ga shugaban, yana ganin abin farko da za a yi don cin gajiyar tattalin arzikin sai an bunkasa ilimi.

“Wannan ya sa ya kaddamar da cibiyoyin ilimi da dama a Afirka kuma ya samar da tallafin karatu dalibai da dama a nahiyar.

Ilimi shi ne tushen kasuwanci saboda mai ilimi shi ne mai kirkire-kirkire kuma shi ne ake tafiya da shi,” in ji Naituli.

Fiye da dalibai 14,000 masu hazaka ne daga Afirka suka amfana tallafin karatu na Turkiyya, yayin da akalla masu aikin jakadanci akalla 250 daga Afirka aka ba wa horo ta hanyar shirin tallafin karatu na Turkiyya.

Turkiyya tana amfani gidauniyar iliminta ta kasa da kasa wato Maarif Foundation, cibiyar koyon harshen Turkiyya ta Emre Yunus Institute don samar da ci gaba. Munene ya ce Erdogan ya yi kokari wajen “tallata manufofin Turkiyya a Afirka”.

Kulla alaka mai muhimmanci

Kamar yadda Dokta Edgar Githua, wato masani kan harkokin kasashen waje, rawar da Turkiyya ke taka wa a Afirka ta hada da shirye-shiryen samar da zaman lafiya.

“Afirka muhimmiyar kawa ce ga Shugaba Erdogan kuma kasar tana da karfin kada a ji kan batun samar da zaman lafiya da harkokin diflomasiyya,” in ji shi.

Har ila yau Githua ya yi amannar cewa Turkiyya tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a nahiyar.

“Yarjejeniyar fitar da hatsi na Tekun Bahar Aswad manuniya ce ga irin rawar da Turkiyya take taka wa wajen wadatar abinci a Afirka.

Lokacin da Shugaba Erdogan ya tsawaita yarjejeniyar da wata biyu a watan Mayu, ya ce ya yi hakan ne saboda Afirka.

Rasha da Ukraine su ne kasashen da suka fi noman hatsi a duniya kuma Turkiyya ce ta taimaka wajen wucewa da hatsin ta Tekun Bahar Aswad.”

Policy of non-interference

Githua ya ce Afirka tana maraba da Turkiyya saboda “ba kamar sauran kasashen yamma ba, ita ba ta tsoma baki a cikin al’amuran siyasar cikin gidan kasashen Afirka”.

“Turkiyya ba za ta ce maka wannan ya kamata a matsayin shugaban kasa, ko yadda za ka yi rayuwarka. Suna so ne kawai su yi kasuwanci da kai da kuma bunkasa tsarin rayuwarka,” kamar yadda ya shai da way TRT Afrika.

Masanin kan harkokin kasashen waje ya yi hasashen cewa Erdogan kara fadada tallafin tattalin arzikin da na tsaro da na ayyukan jin kai wadanda take bai wa Afirka a shekaru biyar mash zuwa.

“Kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a nahiyar,” in ji Githua. Alkaluma sun nuna girman dangantaka da ke tsakanin Afirka da Turkiyya.

Akwai akalla ofisoshin jakadancin Turkiyya 44 a Afirka, hakan ya sa ta sahun gaba na kasashe hudu da suka fi yawan ofisoshin jakadanci a nahiyar a bayan China (mai 53) da Amurka (mai 49) da kuma Faransa (mai 46).

A bangaren kiwon lafiya Turkiyya ba za a iya kawar da ido kan gudunmuwar da kasar take bayarwa a Afirka ba. Misali, a babban birnin Somaliya Mogadishu, Erdogan ya gina babban asibiti a shekarar 2015, wanda aka sa masa sunansa.

A Senegal, Turkiyya ta yi gine-gine da dama ciki har da katafaren filin wasa Abdoulaye Wade Stadium mai daukar ‘yan kallo 50,000 wanda kamfanin gine-gine na Summa ya gina a tsawon wata 17 farawa daga watan Fabrairun 2020.

Cheikh Tidiane Gadio, tsohon ministan harkokin wajen Senegal ya bayyana irin rawar da Shugaba Erdogan yake taka wa wajen karfafa dangantaka da Afirka wacce duka bangarori biyu suke amfana.

“Shugaba Erdogan ya samar da wani sabon tsari na hulda da kasashen duniya…ya kawo sabon wani shiri na hulda da Afirka,” kamar yadda Gadio ya shaida wa TRT Afrika.

Shugaba Erdogan ya ziyarci Senegal akalla sau hudu. A Tanzaniya, kamfanin Turkiyya na Yapi Merkezi ne ya yi aikin gina layin jirgin kasa na zamani a kasar. Gwamnatin Ugandan ta yaba wa ingancin aikin.

“Kamfanin Yapi Merkezi yana wani aikin jirgin kasa na zzamani da ya cancanci a yaba masa a Tanzaniya,” kamar yadda gwamnatin Uganda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar 16 ga watan Mayu, yayin da aka sanar da dawo da aikin jirgin kasa Kampala zuwa Kigali.

A Rwanda, wani kamfanin gine-gine na Turkiyya ya gina wani babban dakin taro mai daukar mutum 10,000 a birnin Kigali.

Har ila yau Turkiyya tana wasu ayyukan jin kai a wasu kasashe daban-daban, wanda hukumar Tika ta kasar Turkiyya ta ke jagoranta.

Cude ni, in cude ka

Kamashi da tsaro da sutura da fina-finai da sufuri da kayayyakin aikin soji wadannan wasu bangarori ne da kasashen Afirka da dama suka amfana da Turkiyya.

“Saboda manufofin huldar da muka kulla da Afirka, wadanda suka samo asali daga fahimtar juna da cibiyoyin gwamnati da bangaren ‘yan kasuwa masu zaman kansu da kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyi jin kai, a shirye muke mu taimaka wajen samar da zaman lafiya da daidaito da tattalin arziki da ci gaba a nahiyar.

“Kuma za mu bunkasa alakarmu ba cuta ba cutarwa kuma don amfanin bangarorin biyu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya.

Yayin da zai ci gaba da mulki tsawon wasu shekaru biyar, Afirka ta yi imani cewa shugabacin Erdogan zai ci gaba da kawo ci gaba. Duka bangarorin biyu suna da kwarin gwiwa.

“Akwai wadanda har yanzu suka amincewa da ‘yanci mutanen Afirka. A matsayinmu na Turkiyya, mun yi watsi da son zuciyar da kasashen yamma suke nuna kan nahiyar Afirka.

“Muna hulda da mutanen nahiyar Afirka ba tare da nuna musu wariya ba,” kamar yadda shugaban ya ce a watan Oktoban shekarar 2021.

Alkaluman kasuwanci

A shekarar 2022, Turkiyya ta kai kaya Afirka da kudinsu ya wuce dala biliyan 21 wannan wani adadi ne da ba a taba gani ba a baya. Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ya karu da kaso 12.3 cikin 100 idan aka kwatanta da a shekarar 2021.

Masar ($3.9 biliyan), Morocco ($3 billiyan), Libya ($2.4 billiyan), Aljeriya ($1.9 billiyan) da kuma Afirka ta Kudu ($1.6 billiyan) kasashen Afirka da Turkiyya take kai kayanta mai yawa.

Tama da sinadarai da hatsi da man girki da ‘ya’yan itace kayan gine-gine da sauransu wasu kayayyaki ne da Turkiyya take kai wa Afirka.

“Kasuwanci tsakanin Zimbabwe da Turkiyya yana karuwa,” kamar yadda Ministan Kudi na Zimbabwe Mthuli Ncube ya shaida wa TRT Afrika. Kasarsa ta sayo kaya daga Turkiyya da kudinsu ya kai dala biliyan 17 a shekarar 2021, a cewarsa.

Turkiyya tana shigo da danyen man fetur da zinare da karfe da iskar gas da sauransu daga nahiyar Afirka.

Kamar yadda alkaluma daga Hukumar Kididdiga ta Turkiyya kayan da kasar take sayowa daga Afirka ya kai dala biliyan 8.3 a shekarar 2021, kuma danyen man fetur ne ke kan gaba.

“Da wannan nasarar da Erdogan ya samu na sake zabensa, ana saran ci gaban hulda tsakanin Turkiyya da Afirka saboda babu sauyin shugabanci. Nasararsa za ta tabbatar da ci gaba da kara samar da sabbin damarmakin cinikayyar kasuwanci,” in ji Naituli.

Githua ya yi hasashen kara samun manyan tarukan karfafa hulda tsakanin Turkiyya da Afirka a sabon wa’adin mulkin Shugaba Erdogan.

“Zai yi fatan kara bunkasa ayyukan Turkiyya da hadin gwiwa da Afirka. Yanzu nasarar da ya samu ta ba Erdogan damar hada kan kasar, da kara kulla dangantaka da Afirka da fito da sabbin hanyoyin kasuwanci da nahiyar.”

Erdogan ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Mayu bayan samun kaso 52.18 cikin 100 na kuri’un da aka kada yayin da ya doke Kemal Kilicdaroglu wanda ya samu kaso 47.82 cikin 100.

Zaben ya kai zuwa zagaye na biyu saboda babu dan takarar shugabancin kasar da ya samu fiye da kaso 50 cikin 100 na kuri’un da aka kada a ranar 14 ga watan Mayu, duk da cewa Erdogan ne ke kan gaba a zagayen farko na zaben.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here