Yadda aka sayar wa maniyyatan Kano kujerun Hajji na bogi

0
162

Sabon shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano Rabi’u Danbappa ya zargi magabacinsa da damfarar maniyyata da suka biya kudin kujerun Hajji 190 na bogi.

A lokacin da yake karbar jagorancin hukumar a hannun tsohon shugabanta, Muhammad Abba Danbatta a yammacin yau Alhamis, Lamin ya ce, “Na tarar sun sayar da kujeru fiye da wadanda Hukumar Aikin Hajji a Kasa (NAHCON) ta ba jihar.

“A ka’ida Hukumar NAHCON ta ba Jihar Kano kujeru 6,082, amma sai suka sayar da 6,273; Ba ka da abu, bai kamata ka sayar da abin da ba ka da shi ba. Wannan kuskure ne,” in ji shi.

A cewarsa, ya yi kokarin neman karin kujeru, amma Hukumar NAHCON ta shaida masa cewa ba ta da wasu kujeru da za ta iya kara wa jihar.

Ya ce, “Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan, ya ce gaskiya babu kujerun da za su iya kara mana. A yanzu sai su nemi tsohon shugaban Hukumar don neman kudadensu.”

Lamin Danbappa wanda ya taba jagorancin hukumar sau biyu, ya ce, “Ni duk tsawon zamana a wannan hukumar ban taba sayar da kujerun da ba ni da su a hannuna ba, ina tsayawa a kan iyakar kujerun da Hukumar NAHCON ta ba ni.”

Sabon shugaban hukumar ya ce sayar da kujeru fiye da wadanda NAHCON ta bayar ne “Ya sa a bara aka bar alhazan a kasa ba tare da sun tafi Kasa Mai Tsarki ba.

“Amma ni tsawon shekaru takwas da na rike Hukumar 1999-2003 da 2011-2015 ban taba barin alhaji ko daya ba. Idan ka ga mutum bai tafi ba, to sai dai idan matsalar daga gare shi ta taso,” in ji shi.

Sai dai duk kokarin Aminiya ta jin ta bakin tsohon shugaban hukumar a kan wannan magana, ya ci tura, inda ya ja bakinsa ya tsuke.

Amma ya nuna godiyarsa ga Allah da Ya nuna masa wannan lokaci da ya kammala aiki lafiya tare da yi wa alhazai fatan yin Hajji karbabbiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here