Tinubu ya shiga wata ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC a Abuja

0
130

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki a fadar gwamnati da ke Abuja.

Gwamnonin dai sun samu jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda a kwanan nan aka zabe shi matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC.

Cikin wadanda suka halarci taron har da sabbin gwamnoni tara da wasu goma sha daya da suka dawo a wa’adi na biyu.

Akwai dai shawarwarin da ke nuni da cewa ganawar ta kasance karo na farko a hukumance tsakanin shugaba Tinubu da gwamnonin jam’iyyar APC tun bayan rantsar da shi a farkon makon nan.

Batun zaben shugaban nin majalisa na iya kasancewa cikin ajandar taron da batun nadin mukamai da ministoci da kuma Matsalar man fetur da ke tayar da yamutsi a kasar a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here