Dabarun kauce wa raɗaɗin janye tallafin man fetur

0
113

Tun bayan tabbatar da ƙarin farashin litar mai a Najeriya sakamakon furucin sabon Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a jawabinsa na farko cewa ‘batun tallafin mai ya kau’, al’amura ke neman dagulewa a ƙasar.

Lamarin dai ya sa jama’ar ƙasar soma yin karatun ta natsu a wani ɓangare na rage wa kansu raɗaɗin da matakin ya haifar ga harkokinsu na yau da kullum.

Kafin wannan mataki dai, dama tattalin arzikin Najeriya na cikin wani yanayi kasancewar hauhawar farashin kayayyaki na ƙaruwa – ƴan ƙasar kuma na fama da tsadar rayuwa.

A wannan maƙala, BBC ta ji ra’ayoyin mutane kan hanyoyin da suke bi na cimma buƙatunsu na yau da kullum da kuma shawarwarin masana kan abin da ya kamata jama’a su yi a irin wannan yanayi.

Abubakar Ibrahim Kankare Gama, wani mazaunin Kano ne da ya ce matakin da ya ɗauka tun bayan shiga wannan yanayi shi ne na rage kashe-kashen kuɗi ganin yadda kudin mota ya ninka kusan sau uku.

“Na yi ƙoƙari na janye wasu kashe-kashen kuɗi da nake wanda bai zama dole ba, wanda a baya nakan yi su saboda wataƙila na samu rara ta kuɗi, toh yanzu hakan ba zai yiwu na ci gaba da kashe-kashen kuɗin ba,”

“A yanzu na sauke duk kashe-kashen kuɗin da nake, sai mun ga abin da hali ya yi, idan ta kasance an samu gyara a nan gaba, sai mu dawo mu ci gaba da kashe-kashen, idan ba a samu gyara ba a haka za mu ci gaba da tafiya.” in ji Abubakar Gama.

Shi kuwa Jibrin Abdullahi, wani tela da ke Kofare a jihar Adamawa ya ce rayuwa ta yi musu tsada kasancewar aikinsa yana buƙatar amfani da man fetur a injin janareto.

A cewarsa, yanayin da aka shiga ya sa dole ya sake nazari kan farashin ɗinki sai dai ya ce tuni abokan hulɗarsa suka fara ƙorafi game da ƙarin kuɗin ɗinkin da ya yi.

Bello Muhammad shi ma mazaunin Yola a jihar Adamawa ya bayyana cewa zai koma tafiyar da harkokinsa a kan keke ko kuma taka sayyadarsa saboda “idan ka ce za ka sayi mai ka sawa abin hawa, abu ne mai cin kuɗi sosai, idan ka ce ma za ka hau motar haya domin zuwa inda za ka, kuɗin ya ƙaru.”

Hawwa Bukar Kumshe ta ce a nata ɓangaren ba ta soma ɗaukar wani mataki ba amma ta nemi gwamnati ta abin da ya kamata wajen inganta rayuwar jama’a kasancewar Najeriya ƙasa ce mai arzikin mai kuma ‘bai dace a ce muna siyan mai da tsada ba’.

Sai dai wasu na ganin matakin na cire tallafin man babban ci gaba ne ga Najeriya da ma al’ummar ƙasar matuƙar gwamnati ta yi tsarin da ya dace.

Umar Abubakar Musa na da irin wannan ra’ayin inda ya ce “duk wani ɗan Najeriya, idan ya yi la’akari da baɗakalar da ake a ɓangaren mai musamman harkar man fetur, zai ga gwara cire shi,”

“Talaka ba ya ganin amfaninsa, ba yadda za a ce a ƙasa irin Najeriya mai yawan al’umma, talakawa da talauci a ce ana ɗaukan sama da rabin kasafin kuɗin ƙasar ana sa shi a man fetur a matsayin tallafi,”

Ya ƙara da cewa abin takaici ne a ce kuɗin tallafin mai akasari yana amfanar wasu tsirarun ƴan ƙasar ne a maimakon al’umma baki ɗaya.

A cewarsa, gwara a cire tallafin saboda wataƙila gwamnati, kamar yadda ta ce za ta yi, za ta karkatar da kuɗaɗen wajen samar da abubuwan more rayuwa.

Me ya kamata jama’a su yi?

Masana irin su Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce akwai matakai da dama da mutane za su ɗauka domin taimaka wa kansu a irin wannan yanayi na tsadar rayuwa.

Rage zirga-zirga

Farfesa Sheka ya ce matakin gwamnatin dole ne ya janyo ƙarin farashin kayayyaki a don haka ya kamata mutane su rage tafiye-tafiyen da ba su zama dole ba – hakan kuma zai rage zumunci.

Ya ce an ɗauki matakin ba tare da an yi la’akari da albashin ma’aikata ba – “rana tsaka an ninka farashin abubuwan da suke saya, za a iya cewa an ƙara musu talauci.”

“Idan mutum yana iya cika motarsa da mai a baya, yanzu ba ma zai iya ba, idan mutum yana karɓar mafi ƙarancin albashi, hakan na nufin sai dai ko ka hakura da shinkafa ko ka sayi kwano ɗaya zuwa biyu.” in ji masanin.

Tsuke bakin aljihu

Farfesa Muhammad Muttaqa Usman na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ce yanayi ne da aka shiga kamar ba a shirya ba a don haka ya ce akwai buƙatar mutane su tattala kuɗaɗen da suke samu domin biyan buƙatunsu na yau da kullum musamman abinci.

“Sai an rage duk wani abu da bai zama dole ba.” in ji Farfesa Muhammad Muttaqa.

Ya ce matakin zai shafi ɓangarori da dama kamar ilimi da lafiya da sufuri da kuma abinci.

Abin da ya kamata gwamnati ta yi…

A cewar masanan – Farfesa Sheka da Farfesa Muhammad Muttaqa, sun ce akwai hanyoyi da dama da suka kamata gwamnati ta bi domin tallafa wa ƴan ƙasar ganin irin yanayin da suka shiga.

Sauƙaƙa sufuri

Babban mataki da ya kamata gwamnati ta ɗauka shi ne na samar da motocin bas-bas da za su riƙa ɗaukan jama’a a farashi mai sauƙi ba tare da sun ji a jikinsu ba.

“Su ce za a samar da bas-bas da mutane za su riƙa shiga kan kuɗi ɗan kaɗan.” in ji Farfesa Muhammad Muttaqa.

Inganta albashin ma’aikata

A cewar Farfesa Sheka ya kamata gwamnati ta ƙara yawan albashin ma’aikata ya ninka sau biyu domin daidaita ƙarin farashin da aka samu na mai.

“Ma’aikaci da yake ɗaukan albashi ƙayyadadde, a ƙara masa albashi, idan kuma ba a ƙara masa albashi ba, duk wanda yake da hanyar ya yi sata, zai yi sata domin rayuwa za ta yi ƙunci – gwamnati ke nan ta taimaka wajen lalata tarbiyyar mutane ke nan.” kamar yadda masanin ya ce.

A ganinsa, ga waɗanda ba sa aiki, ya kamata gwamnati ta tallafa musu – abubuwan da aka fi saya ana amfani da su yau da gobe a san yadda za a yi ko dai ba a rage musu farashi ba, a tsayar da farashinsu.”

Bayar da basuka masu sauƙi

Farfesa Muttaqa ya shaida wa BBC cewa akwai buƙatar gwamnati ta duba yiwuwar bai wa mutane basuka masu sauƙin kuɗin ruwa ta yadda za su tafiyar da harkokinsu ko kuma kasuwancinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here