Tallafin mai: An tashi baran-baran a tattaunawar gwamnati da ’yan kwadago

0
107

An tashi baran-baran a tattaunawar da aka yi a Fadar Shugaban Kasa tsakanin wakilan Gwamnatin Tarayya da na kungiyoyin kwadago kan cire tallafin mai.

Taron dai wanda ya gudana a dakin taro na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya zo ne bayan furucin Shugaba Bola Tinubu kan cire tallafin da kuma yadda Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya kara farashinsa.

Kungiyoyin na kwadago dai sun shiga tattaunawar ne bisa jagorancin shugaban NLC ba kasa Kwamared Joe Ajaero da na TUC, Kwamared Festus Osifo.

Kazalika, tsohon Shugaban NLC kuma tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole da Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar da Shugabar Ma’aikata ta Tarayya, Folashade Yemi-Esan da Shugaban NNPCL, Mele Kyari da kuma Daraktan rusasshen Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu/Shettima, Dele Alake, da dai sauransu.

Sai dai da suke jawabi bayan kammala taron, shugabannin kungiyoyin kwadagon sun bukaci a dakatar da karin yayin da za a ci gaba da tattaunawa.

Sun ce za a sake wani zaman tattaunawar bayan sun gana da sauran Shugabannin kungiyoyin nasu.

Sai dai sun ce babu wata yarjejeniyar ko fahimtar junan da aka samu sakamakon tattaunawar.

Shi ma da yake jawabi a madadin bangaren gwamnati, Dele Alake ya ce za a ci gaba da tattaunawar a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here