Yanzu-yanzu: Tinubu ya gana da Kyari, Emefiele kan cire tallafin man fetur

0
145

Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da babban jami’in Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) Mallam Mele Kyari, da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a fadar gwamnati da yammacin yau Talata.

Ana kyautata zaton makasudin taron na da nasaba da kalaman Tinubu kan batun cire tallafin man fetur, wanda ya ambata a jawabinsa na rantsuwa a ranar Litinin.

Sakamakon tattaunawa kan batun cire tallafin man fetur, an fara samun layuka a gidajen mai.

Lamarin dai ya haifar da kunci da takaici a tsakanin al’ummar kasar nan.

Tattaunawar da Tinubu, Kyari, da Emefiele suka yi na kokarin ganin an magance matsalolin da kuma samar da mafita mai dorewa kan batun tallafin man fetur da ake ci gaba da yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here