‘Yan bindiga sun kashe mutane 25 a sabon harin Zamfara

0
119

Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata sun kashe mutane 25 a wasu hare-hare guda uku a gundumar Kanoma da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa tun farko ‘yan bindigar sun kama wani fitaccen shugaban ‘yan banga a Kanoma mai suna Dahiru Dangamji tare da wasu mukarrabansa uku a wani dajin mai tazarar kilomita 5 daga kudancin garin Kanoma inda suka harbe su har lahira.

Wani mazaunin garin, Ibrahim Aliyu, ya ce ‘yan bindigar sun dade suna kai hari kan shugaban ‘yan banga da wasu manyan yaran sa.

“Labarin kashe shugaban ‘yan banga ya shiga cikin al’umma. Ba da dadewa ba wasu ’yan banga da dama ne suka taru suka nufi dajin domin tunkarar ’yan ta’addan da ke dauke da makamai tare da daukar fansar kisan shugabansu.

“Amma ‘yan bindigar da aka sanar da cewa ‘yan banga na shigowa dajin sun yi kwanton bauna inda suka harbe 16 daga cikinsu. Sai dai kuma an samu asarar rayuka daga bangaren ‘yan bindigar. Rahotanni sun ce an kashe fiye da goma daga cikinsu. Amma, wannan ba za a iya tabbatar da kansa ba.

“Bayan haka ne ‘yan ta’addan suka koma wani mahakar zinari da ke kusa da unguwar Danzara inda suka harbe wasu masu aikin hako ma’adinai biyar. Gawarwakin ma’aikatan hakar ma’adinai da ’yan banga da aka kashe ana ci gaba da diba daga dajin domin binne su.

“Yayin da nake magana da ku, ana zaman dar-dar a garin Kanoma, inda aka ga wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun nufo garin domin kai hari. Muna kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukar mataki a kansu,” inji Ibrahim.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazeed Abubakar, bai samu ya tabbatar da faruwar lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here