Yunƙurin rushe masallaci mai shekara 700 ya jawo zanga-zanga

0
118

Masu zanga-zanga sun yi arangama da ‘yan sanda game da yunurin rushe wata ƙoƙuwar masallaci a garin Yunnan na China, wanda Musulmai suka fi rinjaye.

Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna dandazon mutane a wajen Masallacin Najiaying da aka gina tun a ƙarni na 13 – aƙalla shekara 700 da suka wuce – a ranar Asabar, wanda ke garin Nagu.

Lardin Yunnan mai ƙabilu daban-daban a kudancin China, na da adadin mabiya addinin Musulunci mai yawa.

China ba ta bin wani addini a hukumance kuma gwamnati na cewa tana ba damar ‘yancin yin addini. Sai dai masu lura da al’amura na cewa ana yawan samun murƙushe mabiya addinai yayin da gwamnati ke son ƙarfafa ikonta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here